Addini
Wata kungiya ta karama sheikh Bala Lau saboda wa’azi akan shan Kwaya (kalli Hotunan)
Advertisment
Wata kungiya Mai fafutukar wayar da kan Al’umma akan illar shan Kwaya a Naijeriya karkashin jagorancin Amb. Adasu Fred T, ta karrama Shugaban Izalar Naijeriya Sheikh Abdullahi Bala lau Saboda Kira da yakeyi a wajen wa’azi da sauran karatuttukan sa da Adena Shan Kwaya.
Kungiyar Mai suna “Youths Against Substance Abuse And CRIME In Nigeria (YASAC)” tace tayi wannan karramawa ce domin Shugaba Sheikh Bala Lau yakan Yi kira Da Babban Murya akan Mimbarin wa’azi kan hana Matasa harma da Tsofaffi Da sudena Shan kwaya.
Sheikh Lau dai yakanyi kira ga Gwamnati Da hukumar hana shan Kwaya (NDLEA) Da Hukumar NAFDAC Su Tashi don kama tare da Hukunta masu shigo Da miyagun kwayoyi Da Gurbatattun abubuwa wadanda suke cutar da Al’umma.
Ga hotunan kamar haka:-
Advertisment
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com