Kannywood

Dandalin Kannywood: Rikici ya barke tsakanin Ali Nuhu da jaruma Rahma Sadau

Labarin da muke samu da dumi-dumin sa yanzu na nuni da cewa masana’antar Kannywood na shirin kamawa da wutar rikici babba bayan da alamu ke nuna cewa babban rikici ya barke a tsakanin jarumar nan da aka kora Rahma Sadau da kuma uban gidan ta watau Ali Nuhu.

Wannan rikicin dai ya far fitowa fili ne sakamakon yadda wasu manya jigogi kuma makusantan jarumi Ali Nuhu din suka fito a kafafen sada zumunta na manhajar Instagram suna aibata jaruma Rahma Sadau da munana kalamai da kuma zagi.

Dandalin Kannywood: Rikici ya barke tsakanin Ali Nuhu da jaruma Rahma Sadau
KU KARANTA: Likitoci sun cire wa jariri dan wata daya hakora

NAIJ.com dai da ta danyi karamin binciken ta ta gano cewa musabbabin rikicin bai rasa nasaba da rashin goron gayyata da Ali Nuhu bai ba Rahma Sadau din ba wajen shirya wani sabon fim din sa Abota da ita kuma take ganin kamar ba’a yi mata dai dai ba.

Shi dai Ali Nuhu tamkar wani bango ne a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood inda yake matsayin yaya ko kuma ma uba ga da yawa daga cikin jaruman fim din musamman ma mata.

Haka ma dai mun samu cewa Ali Nuhu din shine musabbanin shigowa da Rahma Sadau harkar fim kuma shine dalilin shaharar ta saboda sanya ta da yayi a cikin wasu fina-finan sa.

Sources:naijhausa.com

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button