Kannywood

Nafisa Abdullahi Ta mayarwa Da Rahama Sadau Martani

Advertisment

Surutun Da Rahama Sadau Ta Keyi Na Cewar ‘Yan Matan Hausa Film Nada Girman Kai, Tana Jin Haushi Ne Kawai Saboda An Koreta Daga Kanneywood, Inji Nafisa Abdullahi 

Sananniyar ‘Yar wasan Hausa Film Nafisat Abdullahi ta mayar da martani akan kalaman da korarriyar jarumar nan Rahama Sadau tayi akan ‘yan Matan Hausa Film, inda ta zargesu da hassada da girman Kai.

Nafisa Abdullahi ta bayyana cewar, kalaman da Rahama Sadau ta keyi  sambatu ne kawai na jin haushin korar da akayi mata a Masana’antar film, amma duk da haka ya kamata Rahamar ta sani cewar Matan Hausa Film sun wuce da tunanin ta, saboda Mata ne wayayyu masu ilimi wadanda suka fahimci rayuwa.

Indai jama’a basu mance ba, a wata tattaunawa da akayi da Rahama Sadau ta soki lamirin ‘Yan Matan Hausa Film, inda ta bayyana su a matsayin masu hassada da kyashi gami da girman kai, sannan tayi kira ga shugabannin Kungiyar ta Kanney Wood dasu mike wajen magance matsalar. 

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button