Kannywood
An kama Daraktan Fim da sabuwar Bazawara
Advertisment
A na zargin sabuwar Bazawarar wadda ko Idda ba ta kammala ba ‘yar garin Zaria ta gudo zuwa jihar Kano, domin ta fara harkar Fina-finan Hausa na Kannywood.
Kamar yadda Gidan Jaridar Dala FM kano na ruwaito. Mahaifin Bazawarar, ya garzayo jihar Kano, ya kuma nemi hukumar Hisba ta jihar, domin nemanta, inda su ka samu nasarar samun Bazawarar, a hannun wani mai bayar da umarni a fim din Hausa, kuma gidan wata jarumar wasan Hausan.
Wakilin mu na ‘yan, Zazu Ibrahim Abdullahi Soron Dinki, na da cikakken rahoton.
Gashi nan a kasa sai ku saurara domin jin yadda ta kaya.