Shin Da Gaske Al’amin Chiroma Baban Lukman na Labarina Rasuwa?
Yanzu nan majiyarmu ta samu wani labari marar dadi wanda Allah yayiwa daya daga cikin jigon shirya fina finai a Masana’atar Kannywood wanda ya shara a cikin masana’atar Kannywood.
Al’amin Chiroma shine miji ga jaruma Wasila wanda itama tayi tashe sosai a cikin shirya finafinai wanda Allah ya azurtasu da ya’ya inda sunfi shekara goma da aure.
Da yamma ranar Alhamis din nan munka samu wannan labari wani dan jaridar Ahmad Nagudu kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
“Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji’un!!!
Allah Ya yi wa wannan bawan Allah Al-Amin Ciroma (wadda ke fitowa a Baban Lukman a shirin Labarina) rasuwa a yau sakamakon hatsarin mota.
Ciroma, wadda gogaggen dan jarida ne da ya yi aiki da mabambantan kafafen watsa labarai, ya kasance daya daga cikin jagorori a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood. Domin shine ma mai magana da yawun hadaddiyar kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Arewa (wato MOPPAN).
Da fatan Allah Ya jiƙan shi da rahamarSa, Ya sa aljanna makoma da mu gaba daya da ke tafe a hanya. ”
To gashi nan yana magana da bakinsa inda yake karya wannan zance.