Kannywood

Me Ya Hana Jarumi Baballe Hayatu Yin Aure ?

Advertisment

Duk A Cikin Shirin FINA-FINAI, Wanda Jaridar Dimokuradiyya, Ke Daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

Baballe Hayatu yana daga cikin jarumai da suka shafe tsawon shekaru suna sharafin su a masana’antar finafinai ta kannywood, kuma ya taka rawa sosai a cikin fina-finai da dama don haka in har za a fadi jaruman da suka bada gudummawa ta ci gaban harkar fim to shi ma dole a saka shi a ciki don masu magana suna Cewa Dadewa a bariki ma ‘yanci ne.

Baya ga haka jarumin yana da kyakkyawar mu’amala da jama’a, Wanda yana da wahala ka ji kan su da wani cikin masana’antar ko a wajen ta.

Advertisment

To sai dai wani Abu da ya daure wa mutane kai dangane da jarumin shine, sa’anin sa da dama da suke harkar har ma da yaran da suka zo a bayan sa tuni sun dade da yin aure, amma shi Baballe Hayatu har yanzu  shiru ka ke ji ba amo ba labari.

Wannan ya sa jama’a da dama suke tambayar ko me ya hana shi yin aure? Domin a can baya dai sun yi wata boyayiyyar soyayya da Sadiya Gyale, amma daga baya sai abin ya tashi daga soyayya ya koma zumunci.

Tun daga wancan lokacin dai har yanzu ba a kara jin labarin soyayyar sa ba don haka dai masoya suna zuba ido su ga ranar da wannan Gansamemen jarumin zai yi aure tun kafin lokaci ya kure masa.

Me za Ku Ce?

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button