Sports

Man United Da Sauran kulob 2 suna Zawarcin Ronaldo

Kungiyoyi 3 da Dan wasa Ronaldo zai iya komawa a kakar bana


Babban Dan wasa Ronaldo na iya tashi daga Real Madrid

– Kungiyar Manchester United na zawarcin Cristiano Ronaldo

– Haka kuma Chelsea da PSG sun tasa Dan wasan a gaba


Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo na shirin barin Kungiyar Real Madrid. Mun kawo kadan daga cikin Kulobs din ‘Dan wasan zai iya komawa

1. Manchester United

Dama kuna da labarin akwai kishin-kishin din cewa Dan wasan yace so yake ya koma Kungiyar sa na da watau Manchester United inda zai kara haduwa da Jose Mourinho.

2. Chelsea


Roman Abromovich mai Kungiyar Chelsea zai dage wajen ganin shi ya dauke Dan wasan na Duniya daga Birnin Madrid zuwa Kungiyar Chelsea da ke Landan maimakon ya koma Manchester.


3. PSG

Ba mamaki idan Kungiyar PSG ta Faransa ta nemi sayen ‘Dan wasan don kuwa kamar dai Kungiyar Chelsea, Nasir Al-Khelafi yana son ‘Dan wasan kuma yana su na da kudi.

Cristiano Ronaldo na shirin barin Real Madrid bayan an fara zargin sa da kin biyan haraji. Tuni dai irin su Bayern Munchen su kace ba su a wajen zawarcin ‘Dan wasan.

©naija.com

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button