Sports
An Baiwa Ahmed Musa Sarautar Jagaban Matasan Arewa
Advertisment
An Baiwa Ahmed Musa Sarautar Jagaban Matasan Arewa
Kungiyar daliban Arewacin kasar nan sun nadawa dan wasan kwallon kafa Super Eagles Ahmed Musa sarautar Jagaban Matasan Arewa.
An yi bikin nadin sarautar Ahmed Musa wanda ya auri sabuwar amarya a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni, 2017 a lokacin kaddamar da gurin wasansa a jihar Kano.
Taron ya samu halartar manyan mutane ciki har da shugaban wasanni na jihar Kano, Ibrahim Galadima.
Mahaifiyar Ahmed Musa da sauran ‘yan uwansa sun halarci taron a Kano a jiya Alhamis.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com