Kannywood

KANNYWOOD: Ina Murna Da Rahma Sadau Ta Dawo Harkar Fim Din Hausa – Aisha Tsamiya

Tun bayan da kungiyar ladabtar da ‘yan wasan hausa ta sanar cewa ta dawo da jaruma Rahma Sadau kannywood, jarumai da masu kallon fina finan hausa kowa yake faden albarkacin bakinsa.

Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya tabi sahun takwarorinta jarumai wajen bayyana ra’ayinta akan dawowar Rahma Sadau Kannywood.

Acewar Aisha Tsamiya: “Wallahi, nayi murna da farin ciki alokacin da naji Rahma Sadau ta dawo kannywood sabida dana gaba ake gane zurfin ruwa; ma’ana, idan Rahma tayi laifi akoreta to Aisha zan iya laifi akore ni domin dan adam tara yake bai cika goma ba.”

“Bayan haka duk mai kishin ma’aikatar da yake aiki to za’a same shi yana murna idan an samo sababbin ma’aikata. amma idan aka kori abokin aikinsa dole shima ya yi fargabar kada gobe shima akore shi ko akore ta.
Wannan duk misali ne don haka ina murna da Rahma Sadau ta dawo kannywood. kuma inayi mata fatan alkairi akan fim dinta maisuna RARIYA.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button