Uncategorized

FARASHIN HAJJIN 2017 NA NIJERIYA: Sauki Ko Tsada?

FARASHIN HAJJIN 2017 NA NIJERIYA: Sauki Ko Tsada? 

Daga Jafaar Jafaar

A dauri can, zamanin da duniya ke kwance, kudin Naira kudi ne mai matukar daraja a kasashen Turai, Asiya, dama daular larabawa, wanda hakan ya sanya ma’abota tu’ammuli da Nairar suka ribace ta a huldar cinikayya dama kasuwancin kasa-da-kasa.

A irin wancan lokaci, darajar Nairar sama take da kudaden Amurka dana Saudiya, al’umai da dama na haba-haba da ita. Amma abin mamaki, waccan Nairar da ada din tayi wancan tashe, itace yau aka wayi gari kimar ta ta fadi dahar takai ko a kasuwar Agadas akema kallon hadarin-kaji. Kai hatta a cikin kasar Najeriyar, Naira bata da wani mutunci a idanun ‘yan kasar. Kila hakan bai rasa nasaba da watsi da kananan kudaden Nairar kamar su Sulallan Naira Guda da takardun Naira Biyar da Goma da ‘yan kasar sukai. 

Anyi ta korafe-korafe tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da farashin Hajjin bana, wanda bisa al’ada, kimanin jihohi Ashirin da daya na musulmai ne da birnin Tarayya Abuja kan lazimta a kasar Saudiya karkashin kulawar Hukumar kula da aikin Hajjin Musulmai ta kasar Najeriya din wato NAHCON. 

Mahukunta sunyi ta kokarin nusar da al’uma cewa ba wani abu bane musabbabin dadin farashin Hajjin banan illa tsadar da kudin Dala yayi akan Naira, kasancewar kusan kaso Casa’in da Takwas cikin Dari na dawainiyar Alhazai da hukumar NAHCON din kan aiwatar a kasar Saudiyan da kudin Dala ta keyi. Amma duk da haka, wadanda basu iya fahimtar cewa farashin chanjin kudi shine linzamin dakushasshen tattalin arziki irin namu ba, har yanzu suna ta neman karin haske. 

A bara, sa’ad da muke jimamin faduwar darajar Naira, wasu ‘yan Najeriya nan-da-nan suka yi ta ganin baiken masu kokawa kan lalacewar Nairar, har suke gwabin wai “Da tashin Bam gwamma tashin Naira”, wanda kuwa a zahiri, lalacewar tattalin arziki ka iya haifar da rikicin dama tsadar rayuwa. 

A yanzu haka dai, maniyatan aikin hajjin na bana, nata ‘yan dabarun ganin sun gagganda sun nemi cikon kudin da zasu cikkata kudin kujera kan dadin da aka samu, to amma abin tambayar anan shine: Me yasa Alhazan Najeriya zasu biya kudi sama dana maniyatan sauran kasashe?

Haka dai za kayi ta ji; wannan yace kaza, wancan yace kaza, kowa kuma da abinda zaka ji ya fadi. Amma dai cikin wadanda suka yi tsokaci kan wannan lamari, akwai bayanan shugaban kamfanin jigilar jiragen sama na Med-view Alhaji Munnir Bankole, wanda a iya cewa jawabinsa ya bada haske sosai kan wasu batutuwa da suka shigewa maniyata duhu. Matsayinsa na guda cikin masu ruwa da tsaki a sha’anin jigilar Alhazai, kasancewar sa daya shafe sama da shekaru Talatin a harkar zurga-zurgar jiragen sama, Alhaji Munnir shima dai ya bayyana cewa tashin farashin chanjin dai shine ummul-aba’isin din tsadar da ake ganin kudin kujerar Hajjin bana tayi.

 A bayanin nasa, ya nuna cewa a tsarin jigilar Alhazai, a duk lokacin da jirgi ya kwashi maniyata yakai su kasar Saudiya, to idan ya tashi dawowa zai dawo ne tsura, ba tare da pasinja koda guda ba, wanda hakan kadai wani babban daliline da ko ba a gayawa kowa ba, kasan cewa sha’nin jigilar Alhazai ya bambanta dana jigilar passinjoji zuwa wata kasar. Sannan Munnir Bankole yace yayinda aka gama jigilar maniyata zuwa kasar Saudiya, to doka ce cewar jiragen jigilar Alhazai ba zasu zauna a kasar ba, saidai kowani jirgi ya koma kasarsa, harsai ranar da aka tsara za a fara kwaso Alhazai a maido su gida. Ka ga kenan haka jiragen saman zasu dawo Najeriya tsurarsu bada kowa ba, sannan idan lokacin fara dawo da Alhazan ma yayi su koma kasar Saudiyan tsura ba tare da pasinja ba. 

Har ilau dai, a kowani zuwa, duk kamfanin jirgi sai an caje shi dalar Amurka Dala Dubu Shida (sama da Naira Miliyan Biyu), matsayin harajin ketarawa ta sararin samaniyar kasahen Chadi da Sudan, da jiragen Najeriya kan ratsa kan suje kasar Saudiya. 

Duk da haka, wasu sunyi ta tambayar cewa to ta yaya kuma maniyata na kasar Pakistan kan biya kasa da farashin da maniyatan Najeriya ke biya, duk da kuwa suma sukan ratsa ta wasu kasashen kafin suje kasa mai tsarkin? Anan ma dai wani babban jami’i dake da masaniya kan hakar ya bayyana cewa ita kasar Pakistan takan ci moriyar afuwar biyan irin wancan haraji ne daga kasashen da take ratsawar, saboda wasu dalilai na huldar jakandancin kawancenta da kasashen da take ketarawar. 

To me yasa kuma Alhazan da suka biya a jirgin yawo wato intanashina, suka fi samun rangwamen farashi kasa dana Alhazan da suka biya ta wajen hukuma wadanda ake kira da Piligirims? Ba wani dalili bane illa adadin kwanakin da Alhazan Piligrims keyi a kasar Saudiya ya linka adadin kwanakin da Alhazan jirgin yawo keyi a kasar. Domin a yayin da Alhazan Piligirims keyin kwanaki Arba’in a Saudiyan, su Alhazan jirgin yawo baifi suyi kwanaki Goma sha Bakwai ba. Duka wannan kuma, baya da wasu ‘yan hidindumu da hukuma kewa Alhazan Piligirims din wadanda babu ga ‘yan intanashina.

A shekarar bara, duk da cewar farashin canjin ya kasance ne a Naira Dari da Casa’in da Bakwai kan kowace Dala, amma gwamnatin Najeriya sai data sanya tallafin kimanin Naira Milyan Dubu Sittin da Takwas matsayin daunin kudin Hajjin bara. 

Mun sani cewar kasafin Najeriya na bana an girke shi ne akan Naira Dari Uku da Biyar kan kowace Dala guda. Don haka idan ka lissafa Naira Dari Uku da Biyar din sau Dala Dubu Hudu da Dari Takwas da Biyar, matsayin kudin kujerar kowani maniyaci, zaka iske yayi dai-dai da Naira Miliyan guda da rabi. 

To amma wani abu da bamu gane ba shine, hatta a wannan farashi fa, gwamnatin tarayya sai data sanya tallafi a kudaden aikin hajjin na bana. Wani babban kusa a gwamnatin tarayyar ya shaida min cewar a banan, saida gwamnati ta biya Naira Dubu Dari Uku da Biyu akan kowani maniyaci don a saisaita tsefewar farashin chanjin dalar ga Alhazai. Wanda kaga idan ka lissafa wancan kudi sau Dubu Saba’in da Biyar adadin yawan maniyatan bana, zaka iske akalla ba akasara ba, gwamnatin Najeriyan sai tayi cikon sama da Naira milyan Dubu Asirin da Biyu daga aljihunta. 

A wannan yanayi Najeriyan ke fama da lalurar shagidadden tattalin arziki; yunwa da fatara a ko ina a kasar, ina ga babu hikima idan aka yi watsi da irin wadancan matsalolin rayuwa da ‘yan Najeriyan ke kokawa kai, aka kwashi kudaden kasa
aka antaya a aikin Hajji kawai saboda a samar da kudin kujerar kasa da yadda aka yanka. Na tabbata ladan ciyar da ‘yan kasa dake da bukata ya dara ladan bada tallafin aikin Hajji, tunda batu ne na rai da ibada. 


Zanyi matukar takaici ace gwamnatin da bata iya samar da tallafin man fetur, ko gari, ko shinkafa ga talakawanta ba, amma ta bige da samar da tallafin aikin Hajji ga masu dashi. Mamaki na ma shine yadda talakan da sai kullum ya fita sannan yake samun na hatsi, amma shine zaka ji shi yana neman wai gwamnatin ta debi kudi ta antaya a rangwamen kujerar Hajji. 

A tafsirinsa kan Sura ta 3 Aya ta 97 a cikin Kur’ani mai girma, cewar Allah madaukaki: “Kuma mun sanya Ziyartar Dakin Kaba’a matsayin rukunan ibada ga mutane ga wanda ya samu iko.” 

Malam Bilal Philips yace an ruwaito daga Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare Shi yana cewa: “Iko anan na nufin isasshen guzuri da karfin tafiya. Don haka, dole musulmi ya zamanto ya wadatu da abinda zai ci da wanda zai bari idan yayi niyyar zuwa Hajji. Idan har sai yayi rance sannan zai samu damar ziyartar dakin Allah, to aikin Hajji bai hau kanshi ba…”

©Rariya

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA