Uncategorized

Wahayin Shedan – Sheikh Yusuf Ahmad Tijjani Guruntum

Wahayin  Shedan !!!

Wannan itace makarantar shedan, Ga fatawoyin da almajiransa suka gabatar masa tare da abinda ya cusa musu na jayayya Don kange mutane daga daukar gaskiya:

Almajirai: Shin yaushe ya kamata a tsaida gemu???

Shedan:    Ana tsaida gemu ne in an tsufa, domin kar ka tsayar da shi ka kasa bashi hakkinsa.

Almajirai: Shin dole Mata su sanya Lullubi? 

Shaidan: Ai dayawa masu sanyawar suna fakewa da shi suyi barna,  Tsoron Allah Ai a Zuciya ya ke ba a Hijabi ba,  In sun matsa da bayanai Ku sanya Please call me,  ko Half Sunnah.

Almajirai : Yaya za a samu nasara kan Masu Da’awah. 

Shaidan: Ku cire musu yi Don Allah,  ku sanya musu son burge Jama’a,  Ku rabasu da yawaita Ibada Sannan Ku cusa musu son Duniya, in kuka ci nasara makamansu na yakar rundunata zai yi rauni. 

Almajirai:   Shin yabon manzon Allah da  kida halal ne??

Shedan:      Kwarai da gaske, An rawaito a rarraunan Hadisin karya cewa lokacin Hijira an  taryeshi da kida tare da ‘yammata suna rawa suna juyi, Wannan salon yana daurin sanya nishadi. 

Almajirai:   Wanda ya bar tufarsa ta wuce idon sau ba don girma kai ba yayi laifi?

Shedan:      Tsoron Allah ai a zuciya ya ke ba wai a tufa ba, Annabi yace Abubakar ba ya cikin masu girman kai, In ka sanya tazarce ne kadai za ka fito dan Birni, domin irin Wannan shiga ta kan sanya a yi maka kallon dan tsanani. 

Almajirai:  Menene matsayin wanda yake satar kudin Gwamnati amma yana sadaka?

Shedan:   In baku sata ba ‘yan kudu za su sata!! Kuma ai sadaka tana tsarkake Dukiya! sannan ai taimakawa Jama’ar ake yi. Ki gina Masallatai Ku taimakawa kungiyoyin addini laifukan za su karanta. 

Almajirai: In muka isar da sakon sai aka kawo mana wasu hujjoji yaya zamu yi??

Shedan:  Ku kalato rubabbun dalilai, ku kaucewa gaskiya, Ku tuhumcesu da kin Manzon Allah,  Ku ce musu ‘yan tsanani, Ku jajirce kan matsayinku sannan kuyi tawilin gangan,  ku tuhumcesu da wasu karerayi sannan ku jirani in karo muku Hujja.

Allah yace cikin Qur’ani “Shaidan ya kan yi wa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button