Ba Wanda Ya Kai Dan Bidi’a Wahalar Banza!!! -Dr Muhammad. Sani Umar R/Lemo
Ba Wanda Ya Kai Dan Bid’a Wahalar Banza:
Allah Ta’ala yana cewa, “Ka ce, ‘Shin in ba ku labarin wadanda suka fi kowa asarar ayyukansu. Su ne wadanda aikinsu ya bace a rayuwar duniya, alhali kuwa suna tsammanin suna kyautata ayyuka ne”.[Al-Kahfi, 103-104].
Magabata sun fassara wannan ayar da cewa, ana nufin Yahudu da Nasara, kamar yadda Sa’ad bn Abi Wakkas (R.A) ya yi. Yayin da shi kuma Sayyiduna Ali (R.A) ya fassara ta da cewa, su ne Khawarijawa.
Imam As-Shatibi ya hade ma’anonin guda biyu, inda ya nuna cewa, ayar tana nufin duk wani mai aikata bid’a a addini, sawa’un a cikin Yahudawa ne, ko a cikin Nasara ne, ko a cikin musulmi ne. Domin duk wanda yake bid’a yana daukan abin da yake yi abu ne mai kyau, tare da cewa, ya kaucewa hanyar da shari’a ta yarda da ita.
Wannan magana ita ce, abin da Imamul Mufassirina Ibn Jarir At-Tabari ya bayyana a tafsirinsa. Allah ya tsare mu da aikin bid’a.
Daga Darulfatawa.com
Allah sakawa Mallam