Uncategorized

MAI HAILA ZA TA IYA TABA IZU GOMA | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Advertisment

Tambaya:?
Assalamu alaikum warahamatullah mallam,wai gaskia ne mace mai haila (period) zata iya rike Alqur’ani izu goma?

Amsa
wa’alaikum assalam,
Abin da yafi zama dai dai shi ne: kar mai haila ta taba ko da wani bangare ne a Alqur’ani saboda hadisin Amru Bn Hazm, wanda wasu malaman hadisin suka inganta ,inda Annabi  s.a.w yake cewa: (kar wanda ya taba Al’qur’ani sai mai tsarki),kamar Albani a sahihi  dha’ifil jam’i hadisi mai lamba ta 13738.

Amma ya halatta ta karanta ta hanyar kallo, saboda hadisan da suka hana mai haila karatun Al’qur’ani ba su inganta ba

Allah ne mafi sani
4/01/2017

Dr jamilu yusuf zarewa

posted by Abubakar Rabiu Yari

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button