Uncategorized

HANYOYIN SHIGA ALJANNAH 30 SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

HANYOYIN SHIGA  ALJANNAH 30

.
Wadannan Hadisai duk
sun tabbata daga
ANNABI S.A.W duk wanda ka dauka zai kai ka/ki Aljannah:-

.

1. ANNABI S.A.W yace:
“duk wanda yayi
sallolin asuba da la’asar akan lokaci, zai shiga
ALJANNAH”
.

2. Duk wanda ya rike
karanta AYATUL
KURSIYYU bayan ko wacce sallah, babu
abinda zai hanashi
shiga ALJANNAH face mutuwa”

.

3. Duk wanda yake karanta suratul MULK
kafin ya kwanta
bacci, zata cece shi
zuwa ALJANNAH”
.

4. Duk wanda yayi ALWALA sannan ya
kyautata alwalar,
sannan bayan ya gama
yace:-

 ASH HADU
ALLA’ILAHA ILLALLAHU WAHDAHU LA SHARIKALAH, WA
ASH HADU
ANNA MUHAMMADAN
ABDUHU WARASULUH’
za’a bude
masa kofofin ALJANNAH guda takwas, ya zabi ta
wacce zai
shiga”

.

5. Duk wanda yayi sallolin NAFILA goma
sha biyu a dare da yini, Allah zai gina
masa gida a ALJANNAH”

.

6. Akwai wata kofa a ALJANNAH mai suna
ARRAIYAN,
babu mai shiga ta wannan kofa sai masu
yawan AZUMI”

.
 7. ANNABI S.A.W yace
yaga wani mutum yana
yawo a
cikin gidan ALJANNAH saboda wata BISHIYA
daya sareta akan hanya kada ta
cutar da mutane”

.

8. Duk wanda ya riki
GASKIYA a maganganun sa, zata shiryar dashi zuwa
ALJANNAH”

.

9. Duk wanda ya kiyaye
HARSHEN sa da
AL’AURAR sa, ANNABI S.A.W yace shi kuma ya lamunce
maka ALJANNAH”

.

10. ANNABI S.A.W ya
gayawa sahabinsa kada ka yawaita
FUSHI zaka shiga ALJANNAH”

.

11. Duk wanda yaje
duba MARAR LAFIYA, zai shiga
ALJANNAH”

.
 12. Allah Ya fadi a
Hadisin kudsi, duk
wanda BALA’I yazo masa, karon farko yayi
HAKURI, babu
abinda ya dace dashi
face ALJANNAH”
.

13. Duk MACEN da ta sallaci SALLOLINTA
biyar, ta AZUMCI
watanta, ta kiyaye
FARJINTA, tayi biyayya
wa MIJINTA, zata shiga ALJANNAR ubangijinta”

.

14. ANNABI S.A.W yace,
duk wanda ya
lamunce min ba zai yi
ROKO ba, zan lamunce masa ALJANNAH”

.

15. Wanda yayi
LADANCIN shekara 12
zai shiga ALJANNAH”

.
 16. Duk wanda a
kokarin kare
DUKIYARSA aka kashe
shi, zai shiga ALJANNAH”

.

17. Duk wanda ya toshe wata kofa, a
sahun JIHADI ko
SALLAH, ALJANNAH ta tabbata gareshi”

.

18. Babu wanda zai
MUTU bashi da GIRMAN KAI, HA’INCI,
BASHI face ya shiga ALJANNAH”

.

19. KUNYA na cikin
IMANI, Imani na
ALJANNAH”
.
 20. ANNABI S.A.W yace
duk wanda ya lamunce
masa
abubuwa guda 6, shi
kuma zai lamunce
maka ALJANNAH!

•Duk maganan da zakayi ka fadi GASKIYA,

•ka cika ALKAWARI
idan ka dauka,

•ka bayarda AMANA
idan an amince maka,

•ka kiyaye FARJINKA
•ka rintse IDANUNKA
daga kallon haram

•ka rike HANNAYENKA
daga zalunci”

.

21. Duk wanda ya kewa Iyayensa BIYAYYA zai
shiga
ALJANNAH”
.

22. Duk wanda ya
kasance mai yawan
ALWALA, kuma idan yayi sai ya mata NAFILA
zai shiga ALJANNAH”
.

23. Duk wanda ya
SHAIDA da kalmar
SHAHADA, ya shaida
Annabi Isa A.S bawan Allah ne, kuma Aljannah gaskiya ce,
Wuta ma gaskiya ce,
Allah zai shigar
dashi ALJANNAH
gwargwadon aikin shi”

.
 24. Duk wanda ya zamto mai daukan
nauyin MARAYA, zai
kasance tare da ANNABI
S.A.W a ALJANNAH”

.
 25. Duk mai saukin kai
wajen saye da sayarwan sa, Allah
zai shiryar dashi
ALJANNAH”

.
 26. Duk ALKALIN da
yasan GASKIYA yayi aiki
da ita, zai shiga ALJANNAH”
.
Wadannan kuma bacin yan Aljannah ne kuma
Shahidaine:-

.

27. Duk wanda gini ya fado masa ya MUTU”

.
 28. Duk wanda CIWON
CIKI ya kashe shi”

.

29. Duk wanda
ANNOBA tayi ajalinsa”
.
 30. Duk wanda ya nitse
a RUWA ya zamo
ajalinsa”
ALLAH yabamu dama
da ikon aikatawa Daidai


Allah yasa mu muna daya daga ciki wadanan mutanen

Dan Allah ka turawa yan uwa musulmi a Facebook ko whatsapp


posted  Abubakar  Rabi’u

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button