Uncategorized

HUKUCIN BIN MASABUKI SALLAH|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCI BIN MASABUKI SALLAH Tambaya : Assalamu alaika 

warahamatullah  mallam.

Shin ya halatta abi wanda bai samu cikakken jam’i ba sallah?Misali,na zo masallaci na taradda jam’i na sallar asr saura raka’a 2, da aka idar na mike tsaye don karasa raka’a 2 da ta ragemin, sai ga makararre ya sake hada jam’i da ni.

Shin wannan jam’in na 2 ya halatta? Idan ya halatta,tare da hujjoji. Amsa :

To dan’uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas’alar zuwa zantuka guda biyu :
Malaman Hanafiyya da Malikiyya, sun tafi akan haramcin hakan, saboda ba’a samu magabata suna yi ba, sannan kuma shi masabuki ba liman ba ne, Annabi s.a.w.


kuma ya yi umarni da bin liman ne kawai, sannan hakan zai iya jawowa sallah ta yi karewa, tun da wanda ya bi masabuki, shi ma in ya gama yana ramako wani zai iya zuwa ya bi shi, don haka sai ya haramta . 

Duba Fathul-kadeer 1277 da kuma Mawahibul-jalil 4489.


Malaman Shafi’iyya da kuma Hanabila a mafi ingancin zancensu, sun tafi akan halaccin hakan, saboda hadisin Ibnu Abbas lokacin da ya ga Annabi yana sallah da daddare sai ya bi shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta :666,

A wannan hadisin za mu fahimci cewa ya halatta mutum ya zama liman a tsakiyar sallah, ko da kuwa bai yi niyyar hakan ba tun daga farko, tun da Annabi s.a.w bai hana Ibnu Abbas ba lokacin da ya bi shi, tare da cewa ba su fara da shi ba, sannan kuma duk lokacin da masabuki ya rabu da liman to yana daukar hukuncin mai sallah shi kadai ne,

don haka sai ya halatta a bi shi .
Duba Nihayatul-muhtajj 2233 da kuma Insaf 236.

ZANCEN DA YA FI INGANCI SHI NE ZANCE NA BIYU SABODA ABIN DA YA GABATA DA KUMA HADISAN DA SUKE NUNA FALALAR SALLAR JAM’I.
Allah ne mafi sani .

  Amsawa
Dr.jamilu zarewa
posting  by Abubakar Rabiu Yari
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button