Sansanin wanda sojojin ruwa na Nijeriya suka gano shi a wani gari da ake kira Okpokwu, an yi nasarar kama matasa sama da 20 da aka gano a cikin sa, sannan kuma an gano adduna da makamai da kuma hoton shugaba Buhari, na gwamnan jihar Benue da kuma na wasu manyan hafsoshin sojoji.