Zaben Nijeriya Ya Zama Iya Kudinka Iya Shagalinka -Shehu Sani


Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Nijeriya Sanata Shehu Sani
Tsohon dan majalisar tarayya, Sanata Shehu Sani ya ce har sai an gyara tsarin zaben kasar nan domin hana sayen kuri’u,amma idan ba a dauki wani mataki ba Nijeriya zabe a Nijeriya zai zama kamar cin Kasuwa.
Shehu Sani ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X a ranar Lahadi yayin da yake mayar da martani kan rahotannin sayen kuri’u da suka kawo cikas a zaben gwamnoni da aka gudanar ranar Asabar a jihohin Imo, Kogi da Bayelsa.


Jaridar tashar Liberty tv na ruwaito Jami’an tsaro sun kama wasu ‘yan siyasa a ranar Asabar bayan da aka kama su da makudan kudade, ana zarginsu da sayen kuri’u.
A cewar Shehu Sani, idan kasar ta ci gaba da tafiyar da tsarin dimokuradiyya da ke karfafa sayen kuri’u, masu kudi ne kawai za su ci gaba da mulki.
Sanarwar ta ci gaba da cewa,matukar za mu gudanar da tsarin dimokuradiyya wanda zai karfafa tare da amincewa da yin amfani da kudi wajen siyan kuri’un wakilan jam’iyya da kuma sayen kuri’un al’umma.
To zabe a Nijeriya zai kasance ne kawai ga mutanen da za su iya zuba kudadensu su sayi kuri’u ba tare da wata matsala ba.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)



