Kannywood

Rarara da Aisha Humaira sunyiwa baba karkazu goma ta arziki

Advertisment

Rarara da A’isha Humaira sun baiwa baba karkazu kyautar dubu dari ukku 300k

Majiyarmu ta Hausaloaded ta samu labarin shima shahararren mawakin nan da jaruma aisha Humaira taimawakawa Babba karkazu tsohon jarumin Masana’atar kannywood da ya samu lalurar makanta da kuma talauci inda fitaccen dan wasan kwallon kafa Ahmed musa ya yayi saya masa gida na Naira miliyan biyar 5million da kuma zunzurutun kuɗi domin wasu hidima naira dubu dari biyar 500,000 to shine majiyarmu ta ruwaito cewa suma dauda kahutu Rarara da abokiya aikinsa aisha Humaira zasu taimaka masa.

Humaira ta shaidawa Zinariya cewa tayi shirin hada Mai taimako daga gurin Abokan Aikin ta Yan kannyhood Dan su Siya mishi gida sai taji labari dan wasan kwallon kafan Najeriya Ahmad Musa ya Siya mishi gida, daga nan ne tace duk mai bukatar taimakon Baba karkuzu yaje ya saka a account lambar Baba Karkuzu da aka saka a vedio neman taimakon da Zinariya TV ta saka a shafin ta na Facebook.

Rarara da Aisha Humaira sunyiwa baba karkazu goma ta arziki
Rarara da Aisha Humaira sunyiwa baba karkazu goma ta arziki Hoto: Facebook

Ta Kara da cewa bayan nan ba Wanda ya turo mata da ko sisi bayan Wanda Mai gidan ta Rarara ya bayar suka hada.

Haka Zalika tayi wa Ahamad Musa Godiya da namijin kokari dayi.

Har wa yau dai za’a ce Aisha Humaira itace Wanda tayi abun a gani a kannyhood wajan nemawa baba karkuzu taimakon da Tashar Zinariya ta wallafa.

Har yanzu kofar cigaba da taimakon Baba a bude take, an siyawa baba Gida Amma yanzu Yana bukatan taimakon kayan Abinci da na kula da lafiyar shi.

Daga karshe Dai Baba karkuzu yayi Godiya ga dukka Wanda suka turo Mai taimako yace Allah ya biyasu abun da suka Mai a duniya da lahira.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button