Labarai

Ganduje ya baiwa Dangote, Abdussamad, Dantata muƙami

Advertisment

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Aliko Dangote, Aminu Dantata da Abdussamad Isyaku Rabiu a matsayin mambobi na kwamitin gudanarwa na Hukumar Zakka da Hubusi ta Kano.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya baiyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.Ganduje ya baiwa Dangote, Abdussamad, Dantata muƙami
Garba ya ce Dakta Ibrahim Muazzam Maibushira, shi ne a ka naɗa a matsayin Shugaban kwamitin.
Sauran, a cewar Kwamishinan, sun haɗa da Dakta AbdulMutallab Ahmed a matsayin Kwamishina I sai kuma Dakta Lawi Sheikh Atiq a matsayin Kwamishina na ll a hukumar.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa Sauran sun haɗa da wakilan Masarautar Kano, wakilan Ma’aikatar Yaɗa Labarai, Wakilan Ma’aikatar Harkokin Addinai, sai na kasuwannin kurmi, Rimi, Kwari da Singa.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button