An sanya Ranar mukabala Tsakanin Malaman kano da Abduljabar kabara


Gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta sanya ranar da za a tafka mukabala tsakanin fitaccen malamin nan Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da wasu malaman jihar.
Kwamishinan harkokin addinai na jihar Muhammad Tahar Adamu wanda ake kira Baba Impossible ne ya bayyana haka ranar Alhamis a tattaunawarsa da BBC Hausa.
Ya ce za a gudanar da mukabalar ce ranar Asabar 10 ga watan nan na Yuli a Hukumar Shari’a da ke birnin na Kano.
A cewarsa tuni ya mika takardar gayyatar yin mukabalar ga malamin da malaman da za su fafata da shi.
TALLA
Kwamishinan ya bayyana haka ne kwanaki kadan bayan shugabannin zauren hadin kan malaman Kano sun zargi gwammatin jihar da “jan kafa” game da zaman tuhumar suka ce za su yi wa Sheikh Abduljabbar a kan zargin cin zarafin Manzon Allah (SAW) da Sahabbansa. Ya sha musanta wannan zargi.
A ranar Laraba ne wata Babbar kotun Kano ta amince da bukatar lauyoyin Sheikh Abduljabbar kan sauraren hujojinsu na neman soke umarnin wata kotun Majistire da ke jihar na rufe masallaci da makarantar malamin.
Alkalin kotun, Mai shari’a Nura Sagir ne ya bayar da umarnin, bayan la’akari da korafin da malamin ya yi na rashin ba shi damar kare kansa daga wasu zarge-zargen da ake yi masa.
Da ma dai Sheikh AbdulJabbar ya bayyana dakatarwar da gwamanatin ta yi masa daga yin wa’azi da rufe masallacinsa da cewa “zalunci ne”.



