Labarai

Ibrahim Attahiru: Babban hafsan sojin ƙasa Na Najeriya ya Rasu

Advertisment

Babban hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya rasu sakamakon hadarin jirgin saman soji a Kaduna.
Mai magana da yawun rundunar sojin, Birgediya Janar Mohammed Yarima ne ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin.
Bayanai sun ce jirgin saman na soji ya fadi ne a kusa da filin tashi da saukar jiragen sama na Kaduna kuma mutum takwas ne a cikin jirgin lokacin da lamarin ya faru.
Rundunar sojin saman Najeriyar ta wallafa wani saƙo a shafinta na Twiiter inda ta bayyana cewa wani jirginta ya faɗi a kusa da filin jirgin sama na Kaduna.


Laftanar Janar Ibrahim Attahiru shi ne ya maye gurbin Janar Tukur Buratai babban hafsan sojan ƙasa.
An haifi Janar Attahiru a 1966 a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Kafin ba shi wannan muƙamin, Laftanar Janar Attahiru shi ne shugaban runduna ta 82 a rundunar sojin Najeriya.
Ya taba jagorantar yaƙi da ƙungiyar Boko Haram amma a shekarar 2017 ne Janar Tukur Buratai ya sauke shi daga muƙamin bayan wasu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai inda aka kashe wasu mutane 50 a lokacin da suke sallah a masallaci.
Dama dai Buratai ya ba shi wa’adin kamo shugaban Boko Haram Abubakar Shekau a mace ko a raye.
Janar Nicholas Rogers ne ya maye gurbinsa.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button