‘Yan bindiga a jihar Neja dake Najeriya sun fille kan wasu manoma guda 10
Rahotanni sun ce, baya ga wadanda aka kashe, wasu kuma sun samu raunka daga harin ‘yan bindigar.
Bayani sun ce ‘yan bindigar sun kuma yi garkuwa da wasu mutane cikin su harda wani ‘dan kasar India.
Mazauna yankin sun koka kan yadda maharan ke musu kisan-gilla.
’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Wayam da Belu-Belu a Ƙaramar Hukumar Rafi da ke Jihar Neja, inda suka kashe aƙalla manoma 10, ciki har da mata, sannan suka sace wasu.
Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa an sare kan mutum shida daga cikin waɗanda aka kashe.
Hakazalika sun ce maharan sun jikkata wasu da dama.
Bala Tukur, ɗaya daga cikin mazauna yankin, ya bayyana cewa, “Sun kashe mutum 10 ba tausayi. Kowa ya tsere. Samun damar girbe amfaninmu yanzu zai yi wuya.”
Harin ya kawo cikas ga aikin noma a yankunan, inda wasu mazauna yankin aka tilasta musu biyan kuɗin haraji kafin shiga gonakinsu don girbe amfanin gona.
’Yan bindigar sun kuma kai hari garin Zungeru inda suka sace mutane da dama, ciki har da Indiyawa biyu da ke aiki a gonar shinkafa a Borgu.
Gwamnatin Jihar Neja, ta sanar da cewa tana sane da lamarin, inda Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed ya yi ƙarin haske kan lamarin.
Ya ce, “An tura jami’an tsaro domin su magance matsalar da kuma hana ta sake faruwar hakan a gaba.”
Wani mazauni gari Mbb kagara da hausaloaded ta samu ya bayyana cewa a karkashin martanin dan jarida Ahmed Tijjani Ramala yana mai cewa:
Oga a garinmu abin ya faru
Sundai yanke kawunansu ammah basu tafi da kawunan bah
Sun dora kawunan a saman qirjinsu, sannan sun tafi da wasu da dama Mata da yara
Yanzu haka da Nike maganar nan sun sake gangarowa a wannan yankin
Kuma har yanzu babu wani agaji daga mahukunta
Tsakanin kauyen dakuma inda camp din sojoji suke be wuce kilometer 1 bah
Allah kawo mana mafita kawai