Labarai

Dalilin da ya sa aka kori Seaman Abbas daga aiki — Rundunar Soji



Rundunar tsaro ta kasa a Najeriya, ta yi ƙarin bayani game da dalilan sallamar sojan ruwan nan Seaman Abbas Haruna daga aiki.

A wajen wani taron manema labarai da ta kira a Abuja, hedikwatar tsaron ta ce an sallami Seaman Abbas daga aiki ne bayan wata kotun soji ta same shi da wasu laifuka uku da ake zarginsa da aikatawa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar tsaron ta Najeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya shaida wa BBC cewa, Seaman Abbas, ya yi wasu abubuwa na rashin ɗa’a.

Abubuwan sun hada da kin bin umarnin kwamandan bataliya da kuma yin surutu a lokacin da kwamandan ke jawabi ga sojoji.

A cewar Gusau, da kwamandan ya umarci Abbas ya kai kansa wani ɗaki da ake tsare mutane idan sun yi laifi sakamakon kaifin da ya yi, to sai yaƙi zuwa.

“Daga nan ne sai kwamandan ya ce tun da yaƙi zuwa to a karɓe bindigar dake hannunsa, to maimakon ya miƙa bindigar sai ya fara harbe-harbe har sai da fitar da harsashi 16, to Allah ya kiyayye bai harbi kowa ba”.

Tukur Gusau, ya ce a ɓangaren aikin soja ba a wasa da batun bindiga ko harsashi, domin harsashi ɗaya idan soja ya fitar sai an bibiya an ga me yasa ka fitar da shi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar tsaron ta Najeriya, ya ce, “Bisa ga wannan aka tuhumeshi inda aka tura shi kotun soja kuma koda aka kai shi ya amsa laifinsa, a kan haka ne kotu ta tuhumeshi da aikata laifuka uku”.

Ya ce a watan Fabrairun 2023, kotun ta kore shi daga aiki.









Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button