Kannywood

Da ɗumi-ɗumi: Mawaƙi Ali Jita ya cire Jar Hula ya fice daga NNPP Kwankwasiyya zuwa APC

Mawaƙi Ali Jita ya cire Jar Hula ya fice daga NNPP Kwankwasiyya zuwa APC ta hannun Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Barau Ibrahim Jibrin.

Jita dai yana cikin jiga-jigan Ƴan Kwankwasiyya daga masana’antar fina-finan Hausa, shi ne ya yi fitacciyar waƙar nan ta ‘Abba Gida-gida Abba ne…’.

Da ɗumi-ɗumi: Mawaƙi Ali Jita ya cire Jar Hula ya fice daga NNPP Kwankwasiyya zuwa APC
Ali Jita & Sanata Barau

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Sanata Barau ke ci gaba da yiwa Ƴan Kwankwasiyya tsamen nama.

Ko a kwanakin baya ma Sharu Habu Tabule da Rabi’u Daushe sun fice daga Kwankwasiyyar zuwa APC gidan Barau.

Da ɗumi-ɗumi: Mawaƙi Ali Jita ya cire Jar Hula ya fice daga NNPP Kwankwasiyya zuwa APC
Ali Jita & Sanata Barau

A gefe guda kuma ana ta samun masu kokawa da tsarin da ƴan Kannywood na Kwankwasiyya ke ciki, kamar su Jarumi Garzali Miko da Jaruma Hafsat Muhammad da Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya fina-finai ta Ƙasa Malam Salisu Officer sun fito sun koka.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button