Jaruma Fati Nayo Kyauta Dillaliya ta fito takarar Kansila
Fitacciyar jaruma a masana’antar Kannywood, Fati Nayo Adam wacce aka fi sani da Kyauta Dillaliya ta bayyana dalilin da yasa ta yanke shawarar neman kujerar Kansila a zaben kananan hukumomi dake tafe a ranar 26 ga watan Oktoba a jihar Kano.
Kyauta Dillaliya, wacce ke fitowa a shirin Dadin Kowa na tashar talabijin ta Arewa24 ta bayyana hakan ne a yayin tattaunawar da jaridar Daily News 24 a yau Laraba.
Jarumar, wacce ke takara a karkashin jam’iyyar NNPP, ta ce ta shiga siyasa ne da kuma tsayawa takara don taimakawa al’ummar mazabarta ta Dorayi a Ƙaramar Hukumar Gwale.
“Muna da matasa da dama a cikin al’ummar mu wadanda basu da aure da kuma ba sa iya tallafawa mata saboda basu da aikin yi. Na fahimci cewa, hanya daya tilo ta taimakawa mutane, shi ne shiga siyasa”, inji ta.
” Na lura wasu matasan, suna da aikin yi amma basu da gidajen da zasu ajiye matan. Don haka nake son siyan fili, inda za a gina dakuna da bandaki domin baiwa matasan inda zasu yi aure su zauna da matayensu.
“Zan kuma tallafawa wasu matasan da kayan noma. Domin noma ita ce tushen arziki. Bugu da kari zan taimakawa mata da jari”.
Kyauta Dillaliya, wacce tayi ikirarin cewa ta jima a siyasa, ta yi bayanin cewa zata tallafawa almajirai dake yawon bara a kan titi.
Haka kuma, ta ce bata damu da sukar da ake yi kan shigar mata siyasa a Arewa ba inda ta ce ba ita kadai ce mace dake yin takara ba a zaben.
” Na riga na siyi fom din neman takara. Ba a mutu ko ayi rai bane. Abinda nake bukata daga mutane shi ne goyan baya”, inji Kyauta Dillaliya .
Daily Nigerian Hausa