Rufi ƴan bori : Abba Hikima yayi martani akan Yarjejeniyar SAMOA karanta kaji
Bayan cece kuce akan yarjejeniyar SAMOA da ankayi wanda ake zargin akwai LGBTQ wanda ta hada da auren jinsi, madigo, luwadi da sauransu.
Masani Shari’a a Najeriya Abba Hikima ya fadi Wannan yarjejeniya inda anka dosa da kalma wayo.
Ga abinda ya wallafa a shafinsa.
“Gaskiya ne, a yarjejeniyar Samoa babu inda aka ambaci auren jinsi ko yancin LGBTQ. Amma ba anan gizo yake saka ba.
Ko a kasashen Turai da Amurka ba maganar LGBTQ suke yi ba musamman a farko-farkon tafiyar su. Magana ake yi akan sexual rights, sexual orientation, gender identity da sauran su.
Ina tabbatar muku cewa idan ba’a zage dantse an ci gaba da bibiyar gwamnati ba, da sannu wannan yarjejeniyar zata canza matsayar Nigeria akan LGBTQ.
Maganar death penalty ya ishe mu izna. Yanzu yaushe rabon da kaji an kashe masu laifi a Nigeria? Duk da dokokin mu haryanzu basu hana ba.”