Kannywood

Ina ba ‘yan mata da ke sha’awar shiga harkar fim shawara da kada su shiga – Hadiza Gabon

Hadiza Gabon a cikin shirin da take gayyatar fitattu a bangarori daban-daban na Ganin Room Talk Show, ta ce idan mutum ya shiga fim, zai yi suna a duniya da hakan ke sanya bakin mutane ya yi masa yawa na ko da bai yi abu ba, za a ce ya yi.

Jarumar masana’antar ta Kannywood ta ce akwai ma mutane da yawa da ke yi wa ‘yan fim kallon ‘yan marasa tarbiyya.

Wadannan da ma karin wasu hujjoji ne Hadiza Aliyu Gabon ta bayar game da shawararta ga mata masu tasowa da ke son shiga harkar fim a wannan lokacin.,

Ga bidiyon nan ku saurari firar su

Hausawa zasu ce wannan shine gaskiya a bakin masu ita domin kuwa ba hadiza gabon bace ta farko da suke cewa duk masu sha’awar shigowa su dakata ba.

Wato ta nan kawai zaka fahimci mai daki shi yasan inda yake masa yoyo.

 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA