Ba ni da niyyar komawa gidan Sani Danja – Mansurah Isah


Tsohuwar fitacciyar jaruma a masana’atar Kannywood wadda ta taka rawar gani, tsohuwar matar fitaccen jarumi kuma mawaki a masana’atar Kannywood Mansurah Isah tace sam bata da niyar koma gidan tsohon zumanta.
Ana fira da ita a gidan rediyo Dw inda mai gabatarwa yake mata tambaya.
Me kike kewa da sani danja?
Tayi dariya ta nunawa cewa mai gabatarwa yana neman magana a wajen ta ne amma a cikin raha.
Ina maganar komawa gidan sani danja ?
“A gaskiya kana tambaya ta da sani danja ance zo mu zauna zo mu saɓane , amma gaskiya bana kewar komai saboda dai-dai ne bazan iya ja da ikon Allah ba. A gaskiya bana shirin kome kuma baya cikin tsarina ba yanzu ba, kuma ba nan gaba ba, amma kuma mutum bai san ƙaddara sa ba”- inji mansurah isah.
Ina gaskiyar zargin cewa ƴan fim ba su zaman aure?
” A toh ban san inda sunka samu yan fim basa zaman aure ba, saboda a cikin al’umma da ake biliyoyi mu da ko dubu bamu wuce ba ina anka bar sauran , wannan son kai ne da son rai da son zuciya a cikin al’umma “