Kannywood

Sana’ar fim hanya ce ta fadakarwa – Jaruma Z-Pretty

Zulaihat Ibrahim, wadda aka fi sani da Z-Pretty, tana daya daga cikin jarumai masu tasowa a masa’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, duk da cewa ba ta dauki wani lokaci mai tsawo a harkar fim ba, amma a yanzu ta yi fina-finai masu yawa, inda hakan ke nuna cewa, jarumar ta shigo da kafar dama. A hirar da Aminiya ta yi da ita ta bayyana dalilin da ya sa ta shiga harkar fim, yadda ta samu daukaka cikin kankanen lokaci da burin da take so ta cimma a harkar da yadda take kallon harkar fim a baya kafin ta zama jaruma:

Za mu fara da gabatar da kanki.
Sunana Zulaihat Ibrahim, wadda aka fi sani da lakabin Z-Pretty a masana’antar fim ta Kannywood. Ni ’yar asalin Jihar Kebbi ce daga kauyen Rubba, a Karamar Hukumar Danko, don haka asalin iyayena Dakarkari ne a Zuru, mahaifina ma’aikacin Hukumar Kula da Shige da Fice ne, kuma an haife ni ne a 1997.

Na yi karatun firamare a Legas a cikin Barikin Sojoji. Kuma na yi sakandare a Kwantagora, Jihar Neja, sannan na yi Kwalajen Ilimi ta Tarayya (FCE) a Sakkwato. Bayan na gama sai na fara aikin koyarwa, kuma daga baya sai na ci gaba da karatu bayan makarantar da nake koyarwa ta ba ni damar ci gaba da karatu.
A yanzu ina kusan mataki na karshe a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, a takaice dai saura shekara daya in kammala digirina a ABU.
A matsayinki na daliba kuma malamar makaranta, yaya aka yi kika samu kanki a harkar fim?
Eh to, wannan kuma ra’ayina ne, kuma ka san mutum yana tashi da shi tun yana yaro, duk da yake wani lokacin idan mutum ya girma ra’ayinsa yakan canja. Saboda ta yiwu mutum yana karami ya ce yana son ya zama lauya, amma idan ya girma sai ya ga abin bai dace da shi ba, ko wani abu makamancin haka. To, ni ma haka na tashi ina karama da tunanin in zama lauya, amma da na girma sai na zama mai sha’awar tallace-tallace.
To amma sai na ga ba zan iya zama mai tallace-tallace kai-tsaye ba, dole sai na bi ta wata hanya kamar harkar fim, inda idan na samu shiga to zan samu damar tafiya kai-tsaye zuwa wajen da nake son zuwa na tallace-tallacen. Kuma alhamdulillahi, harkar fim ta karbe ni, kuma ina yin alfahari da haka.
A wacce shekarar kika shigo harkar fim?
Na shiga harkar fim ce a shekarar 2017, ka ga ba wani dadewa na yi ba, don ban fi shekara daya da watanni ba, kuma na shigo ne ta hanyar darakta Sunusi Oscar 442, ta nan aka gabatar da ni a kamfanin FKD da sauran kamfanonin masu shirya fina-finai.
Da yake kin ce ke ’yar asalin Jihar Kebbi ce, ko harkar fim ce ta kawo ki Kano?
Kamar yadda na fada maka cewa mahaifina ma’aikacin Hukumar Shige da fice ne to daga Legas aka yi masa sauyin wajen aiki zuwa Abuja, daga baya kuma aka dawo da shi Kano, yau kusan shekara tara ke nan.Don haka sai ya sayi gida a nan Kano muke zaune a ciki, don haka ni a Kano nake zaune tare da iyayena.
Wanne ne fim dinki na farko da wadanda suka biyo bayansa?
Eh, fim din da na fara yi na farko shi ne wani fim mai dogon zango mai suna ‘Zamantakewa’, kuma a wannan fim din da wadansu suka zo lokeshin din suka ga yadda nake aktin sai suka ga na dace da fina-finan da za su yi. Don haka sai na yi fim na biyu mai suna ‘Akushi’, daga nan sai aka ci gaba, inda na fito na fim din ‘Inda So da Kauna’ da ‘Dace Da Masoyi’ da ‘Bakauye’ da ‘Sagegeduwa’ da sauransu, wadanda a yanzu ina ganin za su kai wajen 20 ko fiye da haka.
Yaya kike kallon harkar fim musamman idan kika kwatanta da lokacin baya kafin ki fara?
A gaskiya kamar a baya da ban fara harkar ba, ina kallon ’yan fim ne kawai a akwatin talabijin, amma yanzu ga shi muna tare da su koyaushe, don haka wani lokacin ma sai na ga kamar ba ni ba ce idan na gan ni tare da manyan jarumai har muna kulla wasu harkoki tare. Don haka wani lokaci sai in ji kamar ma mafarki nake yi. Domin a baya ina tunanin yaya ma za a yi in hadu da kamar su Ali Nuhu, yadda yake burge ni da yadda yake aktin dinsa. Sai kuma ga shi muna tare da shi wani lokacin ma idan ban yi abu daidai ba shi ne yake gyara mini.

Kikan fito a fina-finai na ban-dariya da na santimental, ko yaya kike iya sarrafa jikinki ya dace da kowane irin aktin da aka ba ki?
To ka san idan an ce wa mutum jarumi ya zama zai iya yin komai daga abin da darakta ya umarce shi da yi, don haka ni ina ganin babu wani aktin da za ba a ba ni wanda ba zan iya ba. Don ni duk abin da nake yi nakan dauke shi da gaske ne. Don haka ba na saka wasa cikin aikin don haka ba ni da wani zabi na aikin da za a ba ni.
A harkar fim an fi kallonki gwanar iya rawa da waka, ko dama kin koya ne kafin kika shiga harkar?
To, ni ina ganin rawa wata halitta ce da ko mutum bai je makaranta ba zai iya, domin kuwa yanayin rawa a jiki yake, kana zaune za ka yi kuma kana tsaye ma za ka yi. Don haka a yanayina ina ganin zan iya yin kowace irin rawa.
A yanayi na harkar rayuwa, ko kina ba rawa muhimmanci sosai?
To ni gaskiya a rayuwa ta ban dauki rawa da waka wata aba ba, don haka ba na ba su wani muhimmanci. Domin kuwa harkar fa ta shafi fadakarwa, ba rawar da waka ne suke da muhimmanci ba, sakon da yake cikin fim shi ne yake da muhimmanci. Don haka rawar da muke yi ma wata siga ce ta isar da sako don kalaman da suke ciki. Don haka ita rawa zuwa take yi ba haka kawai ake yin ta ba.
Me ya fi ba ki wahala a harkar fim?
Gaskiya ba abin da ya fi ba ni wahala a fim kamar a ce za a kwana ana aiki, don gaskiya ina shan wahala idan aka ce za a kwana ana aiki, musamman idan aka ce ni ce babbar jarumar fim din, saboda yadda za a kwana a tsaye ba hutu.
Rayuwar mata musamman a harkar fim ana kallonta gajeriya ce, domin ke kanki shaida ce kafin zuwanki akwai mata da yawa da suka shahara yanzu an daina jinsu. Wadansu sun bar harkar, wadansu suna ciki amma ba a yi da su. Wane tanadi kika yi wa rayuwarki game da irin wannan yanayi?
To abu na farko dai shi ne tsare mutunci da kuma nuna tsoron Allah a duk inda ka samu kanka. Kuma na dauka a raina cewa na zo ne don in isar da wani sako domin mutane su fahimta su kuma karu. Kada mutum ya shigo da tunanin yana so ya yi suna don ko ba ka bukace shi ba idan ka yi abin da ya dace to za ka samu.
Don haka tsare mutunci da sanin ya kamata shi ne zai sa ka samu matsayin da kake nema. Sannan ba wai na shigo harkar fim da nufin babu aure a gabana ba ne, duk lokacin da Allah Ya kawo mini wanda muka fahimci juna da shi, sai kawai mu yi aure, domin shi aure sunnah ce, domin da iyayenmu ba su yi ba da ba za a same mu ba, kuma su ma burinsu ke nan su ga mun yi auren.
To mene ne sakonki na karshe?
Sakona shi ne, ya kamata mu mata mu rika kula da wanda zai zo wajenmu da sunan zai aure mu, domin kuwa akwai ’yan yaudara sosai, don haka mata a natsu a rika kula.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button