Bello Turji ya saki duk wadanda yayi garkuwa da su kuma ya tuba -Sheikh Gumi
Sananen malamin nan na Najeriya, Sheik Gumi, ya fitar da bayanai akan kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, na jihar Zamfara, Bello Turji.
Sheikh Gumi ya bayyana dalilin yin kiran sa ga gwamnati
A wata hira da aka yi da malamin a kafar talabijin ta Arise News, Sheikh Gumi ya bayyana dalilin sa na yin kira ga gwamnatin tarayya da kafa ma’aikatar harkokin da su ka shafi barayin daji da makiyaya.jaridar LH na ruwaito
Sheikh Gumi yace:
Gwamnati ta yi duk mai yiwuwa wajen sake canja su “. Ba wai ina kira ne cewa a yi musu wani abu na musamman ba, saboda wadannan mutanen an dankwafe su. Babu wanda ya taɓa cewa an dankwafe su. Ina makarantun su, asibitocin su, titunan su, da kuma ruwan shan su suke? Babu abin da suke samu daga kason ƙasa. Wannan tsari ne da aka daɗe ana tafiya akan sa. Wanne tabbaci nake da shi?
Sai ya ci gaba yana cewa:
Munyi magana da su kuma sun fadi koken su, wanda kuma mun sanar da gwamnati.” A shirye suke da su ajiye makaman su. Misali kwamandan barayin dajin na shinkafi, Turji ya saki duk waɗanda yayi garkuwa da su, kuma ya tuba daga aikata duk wani nau’in ta’addanci. Yanzu yankin yana zaune lafiya, abin da mu ke fada shine, zaman lafiya ka iya samuwa kadai ta hanyar tattaunawa
Ga bidiyon hirar da aka yi da shehin malamin:
Sheikh Gumi ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da wata ministiri ta musamman wacce za ta kula da makiyaya a ƙasar nan.
Sheikh Gumi ya yi wa’azin da ya sanya ‘yan bindiga tuba da ajiye makamansu
A wani labari na daban kuma, Sheikh Gumi ya gudanar da wa’azi wanda ya sanya ‘yan bindiga da dama aje makaman su. ‘Yan bindigan sun tuba sannan su ka ajiye makaman faɗan su a sakamakon wa’azin da shehin malamin ya gabatar.
Kusan ‘yan bindiga 600 da shugabanninsu suka amince da zubar da makamansu don wanzuwar zaman lafiya a jihar Kaduna, The Nation ta wallafa.
Sun sanar da hakan ne bayan wata tattaunawa da suka yi da babban malami Sheikh Ahmad Gumi da kwamishinan ‘yan sanda Umar Muri a Sabon Garin Yadi, karamar hukumar Giwa dake jihar.