AddiniLabarai

Shin ya hallata na fara biyawa mahaifiyata hajji kafin ni ?- sheikh Isa Ali Pantami

Advertisment

Assalamu alaikum warahamatullah domin tun ina yaro nake da burin kai mahaifiyata aikin hajji, malam tambaya ta ice shin ya hallata na fara biyawa mahaifiyata aikin hajji kafin na fara tafiya, ko idan banda halin zan iya biyamata aikin umrah kafin nan?

Amsa

Da farko ina yaba maka akan manufa na burin kai Mahaifiyarka aikin hajji Allah ya taimakeka akan wannan manufa , duk mai wannan manufa Allah ya taimake shi, kuma ina maka albishir in sha allah bazaka bar duniya ba sai ka cika burinka.

Magana akan waya dace ya faru zuwa kai ko ita idan arzikin naka ne, anyi tambaya zuwa ga lajamatu da’ima lil muhisil ilmiya wato permanent committee na kasar saudi arabiya wanda manya malaman mu sun zamo cikin member a cikin Committee din irinsu sheikh bin bas rahimahullah, su sheikh abubakar zayd rahimahullah da makamantansu dukkan su, sun zauna a kungiyar sunyi aiki.

A cikin aikin da sunkayiwa sunyi fatawa akan misa’il akan aikin hajji a volume na na goma sha ɗaya, wannan fatawa sun amsata a shafi na saba’in taimakawa iyaye suje suyi aikin hajji wannan al’amari ne mai muhimmanci ,kuma al’amari ne da ake kusan Allah da shi amma shi mutum ƙashin kansa baije ba to shi zuwansa na farko wajibi ne.

Su kuma a lokacin tunda basu Allah ya baiwa kuɗin zuwa din ba to su akansu ba wajibi bane, amma shi da aka baiwa dama wajibi ne, saboda haka a duk tausayin iyaye da mutum yake da shi idan Allah ya ƙaddara kuɗin kujera nawa gare to kai a wannan lokaci ya wajaba a kanka amma su bai wajaba ba.

Kuma a ƙa’ida ta shari’a ana fara gabatar da abinda ya jawaba akan abinda bai jawaba ba.kamar fadin Allah a cikin suratul Ali imran surah aya ta 97, Allah ya wajabta akan mutane aikin hajji ga wanda ya samu iko.

Tambaya a nan kai ne ka samu iko ko babarka?

Amsa
Kai Allah ya bawa , saboda haka wajibcin akan ka yake ba’a kanta ba .

Zaku iya sauraren sauran bayyani a cikin faifan bidiyo.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button