Babban Likita A Ekiti ya mutu yana gwada kwazonsa da matar fasto a otel
Wata majiya ta ce likitan dan kasar ya mutu ne sakamakon jima’i da matar wani Fasto
Shahararren likita a jihar Ekiti ya mutu sakamakon zargin yin lalata da matar wani Fasto a wani gidan otel a jihar.
An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin a Ikere Ekiti. Kamar yadda jaridarmikiya na ruwaito.
Majiyoyi a garin sun bayyana cewa marigayin mai suna Kehinde ya sauka ne a daya daga cikin dakunan otal din tare da matar.
Wata majiya, wadda ba ta son a buga sunanta, ta shaida wa jaridar The Gazette cewa matar faston ta tayar da hankali game da lamarin lokacin da ta fice daga dakin.
Mutumin ya mutu ne a cikin dakin bayan da ya yi jima’i da matar.
“Matar ce ta buga kararrawa bayan ta fahimci cewa ya fadi. Sai da manajan ya garzaya ya kai mutumin asibiti da ke kusa, amma abin takaici da isowar sa ya mutu,” inji majiyar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, inda ya kara da cewa an fara gudanar da bincike kan lamarin.
Mista Abutu ya ce matar da ta riga ta kasance a hannun ‘yan sanda, za ta rika taimaka wa jami’an tsaro wajen bankado al’amuran da suka haddasa mutuwar Likitan.
Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa, “an dauko gawarsa an ajiye shi a dakin ajiyar gawa”.