Labarai

Zaben2023: Kada ku zabe mu idan kun gaji da ganin fuskokin mu – Shugaban majalisar dokoki ga ‘yan Najeriya

Shugaban majalisar dokokin Najeriya, Ahmad Lawan, ya yi gargadin cewa za a iya samun rashin zaman lafiya, idan aka watsar da majalisar dattawan kamar yadda wasu ‘yan Najeriya ke caccakar su.
A madadin hakan, ya kalubalanci wadanda hankalinsu bai kwanta da sanatocin na majalisar dokoki Najeriya ta 9 a yanzu ba, da kada su zabe su a shekarar 2023 idan ba sa son fuskokin nasu.
Lawan Ahmed ya bayyana hakan ne a yau Juma’a 20 ga watan Nuwamban 2020, yayin da yake gabatar da jawabin bude wani taron na manyan ma’aikatan gudanarwa na majalisar dokoki da hukumar kula da majalisar dokokin a birnin Abuja.
Sannan ya bayyana majalisar dattijai a matsayin wacce ta tabbatar da cewa dukkan sassan kasar suna da daidaito a wajen wakilci, ba kamar majalisar wakilai ba, wanda jahohi masu yawan al’umma ke samar da mafi yawan ‘yan majalisa.
Shugaban majalisar, ya kuma yi watsi da hujjar wadanda ke neman a soke Majalisar Dattawan saboda albashin da sanatocin ke karba. Inda yace kasafin kudin shekara-shekara na Majalisar kasa yake da kashi daya cikin 100 na kasafin kudin kasar na shekara 2021.
#OaKTVHausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button