

Babban kwamandan hisbah na jihar kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da kuma shugaban hukumar tace fina finai Es Abba elmustapha sun tattauna da sha’irai masu waƙen yabon fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.a.w) a jihar kano.
Wannan tattaunawa ta samu halarta manya manyan masu yabon Annabi Muhammad (s.a.w) domin kawo gyara da tsaftace kalamai masu ma’ana wajen yin waƙen fiyayyen halitta.


Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa yana cewa :
Waka abu ne da yake da tarihi tun zuwan addinin musulunci wanda ake ta tunani wanene Allah ya fara baiwa fasaha da azancin fara wake domin idan anka dubu tarihi a lokacin jahiliyya zaka samu fitattun mawaka da suke waka waje koɗa garin su, addinin su, al’addarsu ko fito da jarumta ko yiwa mata waka.,
Malam ya kara cewa Allah ya fito a cikin suratul su’arah sura ce a cikin Alkur’ani Allah ya kara fitowa da addini musulunci game da waka inda a ciki a akwai mawaƙan da Allah ya gamsu da su ya aminta da su, saboda azancin su da basirar su wajen ƙoda addini musulunci da kuma kira zuwa gare shi wanda hakan yasa anka samu fitattu s lokacin manzon Allah (s.a.w) akwai Hassan bint sabeet yana daga wadanda manzon Allah (s.a.w) yake cewa baitinka yafi musu ciwo fiye da saran tako bi.
Kai musu farmaki da qasidunka jibrilu yana tare da kai. Shima akwai Abdullahi bint rawaha , ka’af bint zubair akwai kahsah duk wadannan ana kiransu shu’ara’u nabiyyi Sallallahu alaihi Wasallama.- inji sheikh daurawa
Kwamanda Sheikh Aminu Ibrahim daurawa ya fadi abubuwan da sunka sanya a matsayin ka’idoji da idan wake na yabon manzon Allah (s.a.w) bada shi to za’a gabatar da ita a wajen hukuma domin a ladaftar da wanda yayi wannan wake.
Ga bayyani nan a cikin faifan bidiyo.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)







