Labarai

Dangote ya kwashe shekaru 32 ya na mana zagon kasa -BUA

Kamfanin BUA ya mayar da martani a kan zargin bata sunan da ya ce Aliko Dangote ya masa ta kafofin yada labarai, inda ya musanta zarge zargen da kuma karin haske a kan takun sakar da ke tsakanin su tun daga shekarar 1991.

Sanarwar da kamfanin BUA ya gabatar ta ce, sun fara samun matsala da Dangote ne tun daga watan Agustan shekarar 1991, lokacin da suka dauki aniyar bunkasa aikin samar da sikari wanda a lokacin yayi karanci a Najeriya.

Kamfanin BUA ya ce a wannan lokacin ya zama daya daga cikin wadanda suka samu lasisin samar da sikarin, abinda ya sa Aliko Dangote ya tinkare su domin sayen sikarin daga wurin su, amma basu san cewar yana shirya musu zagon kasa ba ne, kamar yadda shafin tashar Liberty Tvr na wallafa.

Sanarwar tace bayan sun kulla ciniki, Dangote ya basu cakin kudi na bankin Societe Generale na bogi, amma da suka je karbar kudi sai suka tarar da babu a bankin, abinda ya kai ga maka su a kotu da kuma rufe kadarorin da suka mallaka sakamakon zagon kasan da suka ce Dangoten ya musu.

Dangote ya kwashe shekaru 32 ya na mana zagon kasa -BUA
Dangote ya kwashe shekaru 32 ya na mana zagon kasa -BUA Hoto/facebook

BUA ya ce wannan ta sa hukumomi suka rufe musu asusun ajiyar bankun su na watanni 3, tare da rufe wuraren ajiye kadarorin su da kuma gwada karfin imanin su.

Kamfanin ya ce bayan wancan takaddamar da suka tsallake, bayan yan shekaru sun bukaci bude kamfanin sarrafa sikari domin inganta harkokin su a Lagos, saboda haka suka tintibi wani da ake kira Usman Dantata kafin Allah Ya masa rasuwa, wanda kawu ne ga Aliko Dangote, inda suka karbi hayar filinsa a tashar ruwan Tincan.

Bayan sun rattaba hannu a kan yarjejeniya tare da sanin hukumar dake kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya ta NPA da kuma biyan hakkokin da suka rataya a kan su, Dangote ya je wurin shugaban kasa na wancan lokaci Olusegun Obasanjo domin gabatar da korafi a kai.

BUA ya ce Obasanjo ya bada umurni soke lasisin filin da kuma mika mallakar sa ga Dangote, matakin da ya kaiga Kawunsa (Usman Dantata) yayi asarar filin, yayin da aka baiwa BUA umarnin barin filin cikin sa’oi 24, daga bisani sanda suka kwashe shekara guda kafin samun wani filin na daban.

Kamfanin ya ce filin da ya mallaka domin kafa wurin sarrafa sikarin sa a Lagos a yau ya fito ne daga mahaifin shugaban su, wanda ya mallaka masa kyauta, abinda ya kai ga daga darajar su ta zama kamfani mafi girma dake sarrafa sikari a Yankin Afirka ta Yamma.

BUA ya ce daga nan kamfanonin su, sun ci gaba da habaka duk da gadar zaren da ake shirya musu suna tsallakewa.

Kamfanin ya kuma kara da cewar a shekarar 2007 lokacin mulkin shugaba Umaru Musa Yar’Adua da ake bukatar bunkasa harkokin samar da siminiti da kuma kawar da mamayar da wasu suka yi a bangaren, an baiwa wasu kamfanoni guda 6 lasisi ciki harda BUA, amma kokarin su na samun inda zasu dinga sauke siminiti a Lagos ya fuskanci matsala, dalilin da ya sa suka karkata zuwa Fatakwal.

BUA ya ce ba karamar adawa suka fuskanta ba har sanda shugaba Yar’Adua ya bada umarni ga ministan sufuri da shugaban hukumar NPA cewar ya zama wajibi a basu damar bada gudumawa a wannan bangaren.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button