Rashida Mai sana’a tayiwa Aminu J town Wankin babbam bargo akan yace basu taimakon yan uwansu
Sabuwar rigima Rashida Mai sa’a ta Caccaki Aminu j town bayan Sukarsu da Yayi cewa basu son taimakon Yan uwansu Yan Fim.
Tsohuwar Jaruma a Masana’antar Kannywood Rashida adamu Abdullahi da akafi sani da rashida Mai sa’a ta maidawa Aminu j town da martani bayan Sukarsu da yayi kan cewa basa son taimakon yan uwansu yan film.
Shafin labarai shine ya kawo wannan rahoto Kamar dai yadda aka sani Aminu j town ya fito ya Caccaki yan Masana’antar Kannywood kan rashin taimakawa wani daga cikin jaruman Masana’antar me suna malam lawal gajere wanda ya kamu da matsalar kafafu har baya iya tafiya.
Inda ya bayyana cewa Jaruma Hadiza gabon, Mustapha nabraska, Da Naziru Sarkin Waka sune kawai suka Taimaka masa, amma irinsu sarki ali nuhu, abale, lawan ahmad tare da dauda kahutu rarara an tuntube su amma a karshe dai sun nuna halin ko in kula akan lamarin.
Hakan yasa rashida mai sa’a ta fito ta mayar wa aminu j town da martani kan sukarsu da Yayi.