Labarai

Matashi a Kano ya kai iyayen budurwan shi kotu saboda zasu aurar da ita ga wani

Wani matashi mai suna Imam yayi karar iyayen budurwan shi a gaban babban kotun shari’an musulunci da ke hotoro a kano, inda yake neman kotun ta hanasu aurar da ita ga wani saurayin daban.”

Matashi a Kano ya kai iyayen budurwan shi kotu saboda zasu aurar da ita ga wani
Matashi a Kano ya kai iyayen budurwan shi kotu saboda zasu aurar da ita ga wani

“Matashin mai suna Imam Mukhtar Dala yayi karar budurwan tashi mai suna Muhassin Auwal Dala da mahaifinta AA Dala, da kakanta Sani Mai Alawayyo, da kuma aminin babanta Alhaji Audu, inda ya nemi kotu da ta dakatar da auran da ake kokarin yimata saboda shine yayi hidiman da zai aure ta.haka kuma ya nemi a hana Muhassin Dala zuwa wurin kowane mutum don daura mata aure.

“Alkalin kotun mai shari’a Isa Salisu kura, ya saurari korafin wannan matashi kuma ya dage sauraron karan zuwa ranan 30 ga nuwamban nan.”

Wani labarin kuma Ƴan sanda sun cafke ɗan shekara 84 ya yi wa ƴar shekara 8 fyade

Yan sanda a Ogun sun kama wani dattijo mai shekaru 84, Stephen Jack, da laifin yi wa ƴar shekara takwas fyaɗe.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana haka a Abeokuta s yau Asabar, inda ya ce wanda ake zargin yana zaune ne a unguwar Okun Owa da ke Ijebu-Ode, kuma ya yi ƙaurin suna a neman ƙananan yara.

Ya ƙara da cewa mahaifin wanda aka kashen ne ya kai rahoton kubucewar Jack ga ‘yan sanda da ya lura cewa ‘yarsa na zubar da jini daga yankinta

Oyeyemi, Sufeto na ƴan sanda, ya bayyana cewa da aka yi masa tambayoyi, wacce a ka yi wa fyaɗen ta shaida wa mahaifinta cewa Jack ya yi lalata da ita.

Ya kara da cewa an kai yarinyar zuwa babban asibitin Ijebu-Ode domin yi mata magani.

Kwamishinan ƴan sanda a jihar, Lanre Bankole, ya kuma bayar da umarnin a kai Jack sashen binciken manyan laifuka domin gudanar da bincike tare da gurfanar da shi gaban kuliya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button