Labarai

Yadda kanin mijina yayiwa “Yata fyade – wata Mata

 

Kanin Mijinta ne ya yi raping yarta karama, aka wayi gari cikin tashin hankali, cikin kuka mahaifiyar ta nemi a kaita asibiti kanin mijin ya ce ba shi da kudi, haka ta dauki yar aka tafi da ita asibiti likitoci suka bukaci dole sai an kamo wanda ya yi aika-aikar, daga karshe jami’an tsaro suka kamo shi aka yiwa yarinyar dinki saboda ya lalata gabadaya, shi kuma kotu ta yanke masa hukunci aka kai shi gidan gyaran hali, sai dai tun da aka yanke hukuncin mijin ke masifa za ta raba masa zumunci ta sa an kama kaninsa, kwanaki uku da yanke hukuncin ya ce mata shi zai yi tafiya, ya tsallake ya barta da yara goma sai da aka yi wata shida bata ji ko labarinsa ba, wahalar ciyar da yayan nan guda goma ta rataya a wuyanta, har da jariri dan sati biyu ya tafi ya barta, don haka ko ina amso bashi ta ke yi domin ta ciyar da yarannan, da wahala ta isheta ta nemi wani abokinsa ta tambayi ina ya ke, yace ai shi sun rabu da shi tuni yana can, ba ta dai saka wannan mutumin a idonta ba sai da aka shekara cif aka kawo shi gida ranga-ranga ba shi da lafiya, babban tashin hankalin yanzu bashi ya mata yawa har an kaita kotu ana neman a kamata a kaita prison, yanzu haka gudu ta ke yi ba ta iya kwana a gidanta, rannan cikin dare ga ruwa aka zo kamata ta gudu,  ta buya wani kofar gida za ta kwana anan,  wani mai shayi ya ganta a titi cikin dare ga sanyi ya bata aron shagonsa ta kwana, yanzu don Allah matar aure tana kwana a shago saboda gudun kar a kamata, ya ya ku ke tunanin rayuwar yaran da ta haifa goma da hakkin ciyarwarsu akanta ya ke, kuma tana gidan ma an yiwa daya daga cikin fyade ina ga bata gidan, kuma babu abinci? Fauziyya d Suleiman ce na wallafa a shafinta na sada zumunta

Ta biyu kuma rabuwa suka yi da mijinta ya ki ciyar da yaransa ta kaishi kotu aka yanke masa hukuncin zai dinga bata wani abu duk wata, to yaki ta yi sintirin kotun har ta gaji ya ki ciyar da yaransa, yanzu ta rasa ina za ta saka kanta saboda masifar babu ga yara.

Ta uku mahaifinta ne tace ba ta taba gani yayi sallah ba ko da azumi kuwa, ga bakin talauci da suke ciki sai su yi sati basu dora abinci ba a gidansu, ga gidan duk ya rushe, ko ina zubar da ruwa yake duk kwanikan gidan sun daye, daga mazan har matan gidan sai dai kowa ya nemi abunda zai ciyar da kansa, babu mahaifinsu da ruwansu, har harkar fim ta so shiga amma ba ta samu an dauketa ba, yanzu don Allah ta yaya za ka samu tarbiyya a wadannan yaran? yaran da suke neman yadda za su rayu ko ta halin kaka.

Daga daran jiya zuwa yau da safe na ji wadannan koke-koken kaina kamar zai fashe, ni na rasa ta ina zamu fara gyara wadannan masifun da ke bibiyarmu, wato ba za ka gane irin masifar da muke ciki ba sai kana sauraran shirin Rayuwa da ‘Yanci na freedom radio, tabbas da nice Barista Badiyya da ke jin irin wadannan koke-koken wallahi da yanzu hawan jini ya kama ni ko ciwon zuciya, Allah dai ya kawo mafita, amma akwai jan aikin a gabanmu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button