sabon Rikici A kannywood: Ali Nuhu Ya Maka Jaruma Hannatu Bashir A Kotu
Rahotannin da “Dimokuradiyya” take cigaba da bincike, ya tabbatar da cewar tauraron masaantar Kannywood Ali Nuhu ya maka jaruma Hindatu Bashir a Kotu bisa zargin cin zarafi.
Mujallar Film wacce ke bayar da wasu daga cikin Labaran masaantar ta Kannywood, ta tabbatar da hakan tare wallafa batun a shafinta.
kamar yadda Mujallar ta wallafa tace Lauyan Ali, wato Salima Muhammad Sabo ta ofishin lauyoyi na M.L. Ibrahim & Co., ta shigar da ƙarar ne a Kotun Majistare mai lamba 58 da ke unguwar Nomansland a Kano.
Rahotanni sun tabbatar da cewar Ali Nuhu ya yi ƙarar ne saboda akasin da aka samu kan aikin wani fim na Hannatu wanda aka yi alƙawari da shi zai yi, amma ya saɓa.
A ranar da aka yi alƙawari da shi zai je ɗaukar fim ɗin, wato 10 ga wannan watan na Oktoba, an tafi aikin ɗaukar fim ɗin, amma sai Ali Nuhu bai samu zuwa lokeshin ɗin ba domin ya yi tafiya, ba ya gari, tare da alkawarin washegari zai halarta.
A saboda haka ne Jarumar ta fusata har ta aikewa Sarki Ali sakwannin kai tsaye.
Daga bisani bayan an tuntube shi sai Jarumin ya ce ko kaɗan shi bai rattaba wata yarjejeniya da Hannatu ba cewa zai yi mata fim ba, kuma shi bai da wata hulɗar kasuwanci da ita da har za ta tura masa tes ta gaya masa baƙar magana wadda ɓatanci ne a gare shi tare da zubar masa da ƙima a idon jama’a, a saboda haka ne ya ke so kotu ta ɗauki matakin shari’a na ɓata suna a kan Hannatu Bashir.
Ya ɗauki hoton tes ɗin da ta tura masa ya maƙala a takardar ƙarar domin kotu ta gani.
A turance, ƙarar da ya shigar ita ce “criminal direct complaint”, wadda zargin babban laifi ne, yanzu haka dai zaa yi zaman sauraren Shariar na farko a ranar 18 ga wannan watan da muke a cikin don jin baasin bangarorin guda biyu.