Labarai

Allahu Akbar : Abunda yayiwa babansa shima Ɗansa Ya masa

Assalamu alaikum warahamatullah wannan wata ƙissa ce wanda duk wani mai sauran imani wallahi sai zuciyarsa ta kada.

wani bawan Allah yace cewa ya tafiya aikin hajji shi da mahaifinsa a lokacin ana tafiya hajji akan dabbobi irin su jaki,rakumi da Dawaki da dai sauransu daya ke tafiyar ba’a tafiya mutum daya saboda sai an hada kungiya domin irin abubuwan da za’a iya haduwa da su akan hanya.

wannan yace shine mai lura da wannan tawaga idan akwai mai buƙata ruwa a bashi wanda bai iya tafiya a tayarda da shi saboda a lokacin shi yana matashi ne, mahaifinsa yana bisa wani rakumi bawan an huta a wani waje ana tafiya ya duba sai yaga rakumin yana tafiya a hanya amma babu mahaifinsa akai hankalinsa ya tashi ya firgita da ya fita da gudu ya tafi a kaffa domin ganin yake idan ya hau doki kaffarsa tafi doki gudu ya tafi yana ta gudu.

Allahu Akbar : Abunda yayiwa babansa shima Ɗansa Ya masa (bidiyo)

sai ya tafi yana ta gudu ya koma a baya sai ya samu mahaifinsa ya tafi zai kama ruwa sai tawaga ta tashi ya samu mahaifinsa yana sallar nafila ya jira mahaifinsa yayi sallama ya kama hannun mahaifin nasa ya sumbata ya sumbata yace baba kayi hakuri wallahi ban san baka kan dabba nan ba muka tafi yanzu abinda nake so ka hau bayana in goyeka mutafi.

suna can suna jiranmu zamu tafi mahaifinsa yaƙi ya masawa mahaifinsa,mahaifin ya hau kan bayansa wannan yaron ya dauki mahaifinsa suna tafiya sai da zuka zo wani waje tsakanin dutsuna gudu biyu zasu wuce kawai sai yaji mahaifinsa yana kuka hawayen mahaifinsa yana zuba a bayansa sai yayi tsammanin ko wani abu ya sami mahaifinsa baba lafiya?.

Baba yace a’a babu abinda ya faru bashin da yake kai nane Allah ya biyamin sai yaron yace baba me ya faru sai yace shekaru arba’in 40 a baya lokacin zasu je aikin hajji na farko zasu aikin hajji shi da mahaifinsa yace a daidai wannan gurin ya dauki mahaifinsa ya goyeshi a bai ,saboda mahaifinsa ya gaji ya goyeshi yana wayo da shi saboda ya gaji yace a wannan gurin shine kaima ka goyeni kana tafiya dani.

yace Nagodewa Allah da ba mummunan abu nayiwa mahaifina ba, da mummunan abu nayiwa mahaifina da yanzu shi nake girba amma da yake na goyeshi kaima gashi kana goyona  inda rashin mutunci nayi masa ko wani rashin biyayya da kaima a yanzu a daidai wannan wuri ina fama da shi Allah Akbar.

Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar wallahi muyi hankali abinda munkayiwa iyayen mu bashi ne yana nan biye da mu Allah ka karemu ,Allah yasa mudace wsallamu alaikum warahamatullah wabarakihu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button