Labarai

Wannan Rayuwa Dame Tayi Kama: An Kamashi Yana Lalata Da Yar Cikinsa

Yansanda a jihar Ogun sun kama wani magidanci dan shekara 46 mai suna Olusegun Oluwole bisa zarginsa da yiwa ‘yarsa mai shekaru 17 fyade shafin Amihad na ruwaito

A cikin sanarwar da kakakin Rundunar ‘yansandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya sama hannu, ta ce, an cafke Olusegun ne bayan yarinyar da wasu da suka yi mata rakiya zuwa ofishin ‘yansanda dake Ibara ta garin Abeokuta ne, sun shigar da korafin na fyade.Wannan Rayuwa Dame Tayi Kama: An Kamashi Yana Lalata Da Yar Cikinsa

Sanarwar ta ce, yarinyar ta ce, a daki daya suke kwana da mahaifinsu, inda a wani dare bayan an yi barci “ya janyo ni ya yi min fyade da karfi.”

Sanarwar ta Cigaba da cewa, Olusegun ya amsa laifinsa bayan da Jami’an ‘yansanda sun bincike shi, inda daga bisani ya nemi afuwar ‘yarsa.

Kwamishinan ‘yansanda na jihar, Lanre Bankole ya bayar da umarnin a tura maganar zuwa sashen binciken aikata manyan laifuka tare da a tura yarinyar zuwa Asibiti don duba lafiyarta

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button