Labarai

Wani mutum ya kwashe duka kayan da ya sayawa budurwarsa ya rabar sadaka bayan ya kamata tana cin amanarsa

Advertisment

Wani mutum zai yiwa budurwarsa tonon silili bayan da ya kwashe duka kayanta ya rabar sadaka bayan ya kamata tana cin amanarsa da wani

Wani makwabcin mutumin ya ce a halin yanzu budurwar bata sani ba domin tayi tafiya tare da abokanta yayin da saurayin ke shirin daukar fansa.jaridar Taskar labarai na ruwaito.Wani mutum ya kwashe duka kayan da ya sayawa budurwarsa ya rabar sadaka bayan ya kamata tana cin amanarsa

makwabcin nasa na cewa “makwabcin nawa ya kama budurwarsa tana cin amanarsa bai ce mata komai ba… ya jira sai da tayi tafiya ita da kawayenta sannan ya dauki fansa ya tattara duka kayan ta,

yanzu haka ya gama kwashe komi da ya sayo mata sannan ya canza gida. Kuma a haka suna ta yin waya bai nuna mata komi ba, har sakonni yake tura mata na soyayya sai ta dawo za ta tarar da abunda yayi mata” inji makofcin mutumin

WANI LABARI: Kwankwaso na duba yiwuwar komawa PDP ya yiwa Atiku aiki –inji Abba

 

Babban hadimin Atiku ya tsegumta cewa da yiwuwar Kwankwaso ya koma PDP yayi wa Atiku Abubakar aiki, “zamu karbi lissafin wahalar da yayi mu biya, sannan yaje yayi dubale a gaban Sardauna

Abban Hajiya ya kara da cewa “Ni matsala ta da yawan masu surutu akan Atiku Abubakar saboda kwankwaso shine, a kwankwasiyyar ma basu isa magana ba.

Lokacin da zamu rufe ƙofa ciniki ya fada da Jagoran nasu basu sani ba, kuma dole a cewa mijin iya Baba”

Zabe kuwa al’ummar Arewa da kudu Atiku zasu zaba, ba zasu yi asarar kuri’ar su a gurin marasa manufa ba.” -Inji Abba

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button