Kannywood

Yes Kawai suke fadi: Bidiyon karamar yarinya a Dubai tana yi wa su Maryam Yahaya turanci

Wani bidiyo ya yi matukar daukar hankula wanda aka ga jarumar Kannywood, Maryam Yahaya, Minal Ahmed, Momi Gombe da wata kawarsu mai suna Maryam su na ta turanci tare da wata karamar yarinya, shafin Real Ado Gwanja na Facebook ne ya ruwaito.

Da alamu sun dauki hankalin yarinyar ne wanda hakan yasa ta kasa hakuri har sai da tayi musu magana.

Kamar yadda yarinyar tace, sunanta Rumaisa inda ta bukaci su gabatar mata da kawunansu daya bayan daya.

Ta ce sun burgeta, kuma zata so sanin daga inda suke. Anan ne su ka sanar da ita cewa daga Najeriya su ke, ita kuma ta fada musu daga Pakistan take.

Ta ci gaba da jan zancen da tsawo har take cewa Najeriya a Nahiyar Afirka take koh?

Bidiyon ya yi matukar daukar hankalin mutane. Amma dai wasu suna ganin bin baki jaruman suke yi don da alamu Minal ce kadai ta iya tabuka turancin dakyau.

Ga bidiyon a kasa:

https://fb.watch/eGs5HpLIOn/

Tsokacin jama’a karkashin bidiyon

Ga tsokacin mutane karkashin bidiyon:

Fadila H Aliyu tace:

“Sai wow wow su ke yi.”

Saman Na Ta’ala yace:

“Mafi yawan masu kwament anan din ma ba turancin suke ji ba duk yan kano ne.”

Yahuza A Hassan yace:

“Zanso ace Musa mai sana’a na nan.”

Umar Attahir yace:

“Wasu na cin baki.”

Bin Isma yace:

“What is your name kawai Maryam yahaya ta sani! Anata zubo turanci sunyi shiru sai yake suke, Minal ce me kokarin amsawa. Su momi sai washe baki ake kamar ana shooting.”

Aliyu Muhammad Bashir yace:

“Alamu sun Nuna Maryam Yahaya da momy befi sau uku-uku su ka je primary school ba.”

Abubakar Muhd Olan yace:

“Minal ce kadai ta iya yaren dakyau, sauran duk bin baki su ke yi. Lamarin ya bani dariya.”

 

[Via]

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button