Rundinar sojin Nigeria ta kori sojojin da Sunka Kashe sheikh Gwani Aisami
Rundinar sojin Nigeria ta kori sojoji guda biyu wadanda ‘yan sanda suka kama da laifin aikata kisan kai, fashi da makami
Sune sojojin da suka harbe babban Malamin Musulunci a jihar Yobe Sheikh Muhammad Goni Aisami tare da yunkurin sace motar Malamin Datti Assalafy na ruwaito
Sojojin masu mukamin Lance Corporals wato Lance Corporal John Gabriel da Lance Corporal Gideon Adamu, amma kafin a koresu daga aiki sai da aka rege musu matsayi zuwa kuratan Sojoji wato Private
Laftanar Kanar Ibrahim Abdullahi Osabo shine Mukaddashin Kwamandan Recce Battalion rundina ta 241 dake da sansani a garin Nguru jihar Yobe inda sojojin suke aiki ya gabatar da korarrun sojojin, sannan ya mikasu wa ‘yan sanda domin a gurfanar da su a Kotu
Aladu sun kashe ragon layya, tabbas ba zasu tsira ba
Muna fatan Allah Ya tabbatar musu da mafi tsananin hukunci
Allah Ya karbi shahadar Sheikh Muhammad Goni Aisami