Crypto currency

Asalin dalilin da ke sanya mafi yawan ƴan crypton arewa ke yin asara

Kasuwancin cryptocurrency kasuwanci ne da ke buƙatar ilimi da bin matakai daban-daban kafin ma mutum ya kai ga fara sayen coin. Sai dai yawancin ƴan Crypton Arewa ba su damu da neman iliminsa ba, wasu ma ganin su ke kawai sa’a ce ke aiki.

Yayin da ka sayi cryptocurrency, za ka yi tsammanin samun riba, idan ka samu ribar nan to ka sani fah wani ya yi asara ne. Ma’ana kasuwanci ne wanda mutane daga sassa daban-daban ke yi, masu saye na burin su saya a farashin mai sauƙi, masu sayarwa na burin sayarwa a farashi mai tsada. Ashe kuwa kasuwancin cryptocurrency kamar yaƙi ne a tsakanin bangarorin biyu (Bull da Bear).

Taya ka ke tunanin za ka yi nasarar yaƙi kawai da sa’a?
Kafin ka yi nasara a yaƙi, dole kana buƙatar ilmi, ƙarfi da tarin hikimomin cin galabar abokin gaba. Maimakon mutanenmu su natsu sosai su fahimci yadda cryptocurrency ya ke da kuma yadda kasuwar cryptocurrency ke aiki. Kashi 70 na wanda su ke tunanin sun iya cryptocurrency za ka samu sun iya saye da sayarwa ne kawai kamar yadda mai Private mota ya iya tuƙa mota.

Hanya mafi sauki ta koyon cryptocurrency shi ne ka fara sayen coin, anan ne za ka koyi shiga kasuwa ka sayi coin ko ka sayar, kamar yadda hanyar mafi sauƙi ta koyon mota shi ne ka mallaki motar. Direban da ya koyi mota saboda yana da mota za ka samu iya tuƙin motar kawai ya iya, amma bai san mota ba. Inda motar za ta tsaya a hanya ba ma zai gane abinda ya lalace ba. Watakila kafin wani abu ya lalace sai ya bada sign na lalacewar, amma da ya ke tuƙin kawai ya iya to sai bayan abin ya lalace kafin ya sani. Kamar haka, ƴan Crypton Arewa su ke, coin na bada sign na faɗuwa amma ba za su sani ba sai bayan ya faɗi. Saboda yawanci muna sayen coin ne kawai don muna da kudin saye ko don mun iya saye, bawai don mun san haƙiƙanin abinda muka saya da kuma halin da farashinsa ke ciki a kasuwa ba.

AMSA Wa KANKA WAƊANNAN TAMBAYOYIN:

Shin ka san haƙiƙanin menene cryptocurrency, ko kuma kawai kana sayensa ne kana sayarwa? Idan ba ka sani ba, taya ka ke tunanin za ka samu riba idan ka sayi abinda ba ma ka san hakikanin menene shi ba?

Shin ka san yadda kasuwannin cryptocurrency (exchanges) su ke aiki a zahiri, ko kuma kawai shiga ka ke yi ka sayi coin ko ka sayar? Ta ya ka ke tunanin samun riba alhalin ba ka san yadda kasuwar da ka ke kasuwanci ke aiki ba?

Shin ka san yadda farashin coin ke ƙaruwa da raguwa, ko kuma kawai kana ganin yana tashi ne yana faduwa? Ta ya ka ke tunanin samun riba alhalin baka san abinda ke sanyawa farashi ya tashi ko ya bada riba ba?

Shin idan za ka sayi coin kana saye ne saboda dogaro da wata alamar da ke nuna farashi zai tashi ko kuma kawai saye ka ke yi ido a rufe? Ta ya ka ke tunanin samun riba idan ba ka san halin da coin ya ke ciki ba kuma ka saya?

Shin kana sayar da coin ne saboda bayyanar wata alama da ke nuni da faɗuwar farashi na zuwa, ko kuma kawai kana sayarwa ne bayan farashin ya gama faɗuwa?

Shin idan an baka signal, kana tambayar lokacin da ya dace ka saya da lokacin da ya dace ka sayar? Domin idan baka tambaya, koda signal din mai kyau ne to har farashin zai tashi ya kuma sauka ba tare da ka sayar ba.

Shin ka iya gane alƙiblar da kasuwa ke fuskanta, ko kuma kawai kana shiga Facebook, Twitter ka ga post ɗin wani ka yi amfani da abinda ya ce ne? A ina ka samu tabbacin abinda ya faɗa yana da hujjar ilimi akansa?

Shin kana da wani takamaiman Trading Styles da ka ke yi ko kuma kawai kana sayen cryptocurrency ka sayar? Ta ya za ka samu riba alhalin ma ba ka da tsayayyen salon kasuwanci?

“Yin kasuwancin cryptocurrency ba tare da ilimi ba kamar tafiya ne ido a rufe, wanda zai yi wuya ba ka afka rami ba”

Mafi yawan coins ɗin da ƴan Arewa mu ka saya mu ka yi asara, rashin iliminmu ne ya sa muka yi asarar ba wai wani ne ya janyo mana ba. Domin ka shi 80 na coins din da mu ka saya sun tashi daga yadda muka saye su, ma’ana har sun ba mu riba. Maimakon mu duba halin da su ke ciki mu ga idan za su sauka mu sayar, sai kawai mu ci gaba da zura masu ido suna wargajewa, sai bayan kuɗaɗenmu sun tsiyaye mu zo muna jin haushin wanda ya bamu shawarar saye.

Wallahi, matuƙar muna son samun riba a kasuwar Cryptocurrency, sai fa mun cire kasala mun nemi ilimin kasuwa.

Don Allah, indai kana cryptocurrency ne kuma kana jin Hausa, koda ba ka mallaki ‘SIRRIN CRYPTO’ ba, to ka yi aro a wajen wanda ke da shi. Na tabbata zai rage maka 70% na asarar da ka ke yi, zai kuma ƙara maka kashi 70% na samun ribarka.

Nasir I. Mahuta

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button