Addu’a Ga Yan Fansho Da wadanda shekarunsa suka haura Hamsin – Dr Bashir Aliyu Umar
AN YI KIRA GA YAN FANSHO SU YI RIKO DA WANNAN ADDU’A.
Babban Malaminmu Dr. Bashir Aliyu Umar (Hafizahullah) a yau ranar 28 ga Ramadan, a zama na karshe na Tafsirin wannan shekara ta (1443) A yayin da ya ke fassarar aya mai lamba ta (62) cikin Suratul Ankabut, watau fadin Allah Ta’ala:
الله يَبْسُطُ ٱلرِّزْقَ لِمَن يَشَآءُ مِنْ عِبَادِهِۦ وَيَقْدِرُ لَهُۥٓ إِنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَىْءٍ عَلِيمٌ
Ma’ana: Allah yana shimfida arziki ga wanda ya ga dama a cikin bayinsa, Ya kuma kuntata masa, Lalle Allah Yana sane da komai.
A cikin jawaban Babban Malamin a karkashin Tafsirin wannan aya, sai ya karanto Hadisin da aka rawaito Annabi (S.A.W) yana cewa:
اللهم اجعل أوسع رزقك علي عند كبر سني وانقطاع عمري
Fassara: Ya Allah Ka sanya yalwar arzikinka da wadatarka a gare ni a lokacin tsufa na da yankewar rayuwata.
A wannan gab’a ne Malam (Hafizahullah) ya yi kira ga wadanda suka ajiye aikin gwamnati (YAN FANSHO) da wadanda shekarunsu suka tafi gangara (50-60) a kan su dage da yin wannan addu’a, domin samun saukin rayuwa, duba da yanayi da suke ciki, ga shekaru sun ja, ga kuma harkar fansho a kasar nan. A lokacin kuma la’alla ga k’ananan yara da ake biyawa kudaden makaranta, ga harkar asibiti, ga harkar ciyar da iyalai abinci.
Malamin ya ce: “Wannan addu’ar ya kamata dukkan wanda ya kai shekaru: 40- 50 ya yawaita yin ta, domin lokacin da shekara (60-65) za ta zo maka, to lokacin ka yi RITAYA.”
Allah Ya sakawa Malam da alkhair Ya kara masa lafiya.
Dangane kuwa da Wannan Hadisi da Malam (Hafizahullah) ya ambato, Hadisi ne da Al-imam Addabarani cikin “Al-mu’ujamul Ausad’, da Al-imam Al-Hakim cikin “Al-mustadrak” suka rawaito shi daga Hadisin Nana Aisha (R.A), cewa Annabi (S.A.W) ya kasance yana yin wannan addu’a da ta gabata.
Al-imam Alhakim bayan ya fitar da wannan Hadisi cikin (Al-mustadrak) Hadisi na (1987) sai ya ce: Hadisi ne mai kyawun Isnadi da Matani (Hasan) Amma wani Marawaici (Isa Bin Maimun) da ke cikin mazajen Hadisin Bukhari da Muslim ba su yi hujja da shi ba. Sai dai na ga Sheikh Albani ya ce, Alhafiz Azzahabi ya ci dunduniyar Al-hakim, ya ce: Ai Isa Bin Maimun ma abin tuhuma ne, ba kawai k’in hujjar Bukhari da Muslim da shi ba abun ya tsaya.
Alhafiz Alhaisami shi ma ya kyautata wannan Hadisi cikin “Majma’uzzawa’id” Juz’i na (10) shafi na (182) Hadisi mai lamba ta (17420) ya ce: Dabarani ya rawaito shi cikin “Al-ausad’ kuma Isnadinsa mai kyau ne (Hasan)
Sheikh Muhammad Nasir Al-albani shi ma a karon farko ya kyautata (Hassana) wannan Hadisi cikin littafin “Sahihul Jami’i” Hadisi na (1255) amma daga baya ya yi kome (Taraju’i) ya ce Hadisi ne mai rauni sosai (Da’ifun Jiddan) inda ya ce: “A karon farko na mak’alewa (Yin Taqlidi) ga Alhaisami na bi shi a kan cewa Hadisi ne kyakkyawa, amma daga baya na gano cewa Hadisi ne mai rauni sosai”. Ya yi wannan bayani cikin “Silsila Da’ifah” Juz’i na uku, shafi na (569) lambar Hadisi na (1385)
Magana mafi karfi da ta bayyana a gare ni, wannan Hadisi ne mai rauni matuka, Ban samu wata hanyar da za ta karfafe shi ba a iya karamin bincike na, da karancin ilimi na, da raunin kwarewa ta, da gajiyawar nazari na.
-Abu Ahmad Ibnu Adiy Al-jurjãni ya ambace shi cikin littafinsa “Al-kamil” yana mai nuni ga rauninsa.
-Haka shi ma Alhafiz Albaihakiy ya raunata shi cikin littafinsa “Adda’awãtul Kabir” Juz’i na (1) shafi na (360) Hadisi mai lamba ta (270) ya ce: Cikin sanadin Hadisin akwai Isa Bin Maimun, shi kuwa MUNKARUL HADIS.
-Haka nan shi ma Alhafiz Ibnul Jauzi, ya ambaci wannan Hadisi cikin littafinsa “Al-maudu’ãt) juz’i na (1), shafi na (181) sai ya ce: “Wannan Hadisi ne da bai Inganta daga Annabi (S.A.W) ba.”
Sai dai wannan babi ne na addu’o’i, a kan yi rangwame, kamar yadda Al-imamun Nawawiy ya yi wata kyakkyawar shinfida a mukaddimar littafinsa: (Al-azkar) Haka kuma ma’anar addu’ar kalau ta ke, sannan addu’a ce mai matukar fa’idah, lalle kamar yadda Malam (Hafizahullah) ya jaddada kira, hakika ya dace ya cancanta a rike wannan addu’a matuka saboda muhimmancinta da cikar ma’anar lafazinta ga bawa. Ko da idan ana bayani da fuskar ruwaya za a ce ba ta tabbata ba.
Sheikh Ahmad Shakir shi har ta kai ya inganta wannan Hadisi ma cikin Mukaddimar “Umdatu Attafsir An Alhafiz Ibn Kasir”
Allah Ya sa mu dace.
Mai Rubutu:
@Musa Muhammad Dankwano.
28 Ramadan, 1443.