Uncategorized

Yadda Malamin Makarantarsu Ya Yi wannan Yaro Masa Wannan Danyan Hukuncin

Labarin da ya motsa min Zuciya…Yaro ne karami wanda a fuska ban yi zaton ya haura shekara 8 ba,amma mahaifin sa ya turo shi Kano almajiranci daga garin Gamawa a jihar Bauchi

Yadda Malamin Makarantarsu Ya Yi Masa Wannan Danyan Hukuncin
Yadda Malamin Makarantarsu Ya Yi Masa Wannan Danyan Hukuncin

Ba Zuwan sa almajirancin ne yafi damu na ba,domin wannan Ai an saba,amma na farko kankantar yaron nan abar dubawa ce, gashi ilahirin jikin sa yayi kaca kaca da tabbai na dukan bulala,gaskiya wanda yayi masa wannan dukan bashi da tausayi kuma bai cancanci ya amsa sunan Malam ba.

A jawabin da yake bani,yaron ya ce Malamin sa ne yake dukan sa saboda idan yaje bara baya kawo masa komai,wai ashe idan an fita bara sadakar farko ta Malam ce.

Yaron yaci gaba da cewar mahaifiyarsa ta rasu kuma mahaifinsa ne ya kawo shi almajiranci,kuma yace bai San unguwar da makarantar tasu take ba, kwana biyu kenan ya fito bara yayi batan kai ya kasa gane makarantar tasu.

Dan Uwan mai unguwar kofar mata mai suna Hussaini shine ya karbi yaron daga hannun wadanda suka tsinto shi. Yanzu haka dai mun hada su da Sani Bundin wani matashi jajirtacce dake tsayawa marasa gata,na kuma hada su da hukumar yaki da Bara ta jihar Kano karkashin Sheikh Muhammad Al Bakri mikha’el domin a dauki mataki na Gaba.
Babban abin takaici ne ace har yanzu a Kano Ana karbar irin wadannan mini minin yaran da sunan an kawo su bara gaskiya bai dace ba.
Yanzu wannan yaron dai ba a nuna masa jin kai ba,bai samu shakuwa da iyaye Ko yan Uwa ba,idan ya girma a titi wa kuke tunanin zai tausayawa?

Barin irin wadannan yara da muke gani suna gararamba a titi babbar masifa ce,WAcce idan ta tunkaro bazata takaita akan wanda ya jawo ta kadai ba,ya kamata mu ribanya kokari wajen yaki da wannan annoba.
Zamanin da da na yanzu ba daya bane, Ina goyon bayan karatun alkur’ani kuma ina goyon bayan hana bautar da kananan yara.”
“Allah ya kawo mana karshen matsalolin dake damun Mu.”
Rubutawa Nasiru Salisu Zango

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button