Uncategorized

Tsoho mai shekaru 80 ya koka a kotu kan matarsa mai hana shi jima’i

Tsoho mai shekaru 80 ya koka a kotu kan matarsa mai hana shi jima'i
Tsoho mai shekaru 80 ya koka a kotu kan matarsa mai hana shi jima’i

Wani tsohon malamin jami’a ya koka a gaban kotu kan batun matarsa mai hanashi hakkinsa
– Malamin ya bukaci kotu da ta tilastawa matarsa amincewa dashi a gadon aurensu kasancewar bata yarda
– Sai dai, matar ta yi alwashin hana shi hakkinsa saboda aikata lalata da yake yi da wasu matan amininsa
Wani tsohon malamin jami’a mai ritaya dan shekaru 80, Farfesa Muritala Haroon, a ranar Alhamis ya fada wa Kotun Al’adu da ke zaune a Mapo, cewa matarsa, Afsat, har yanzu ta ki amincewa da shi, Legit ta ruwaito.
A lokacin da aka ci gaba da sauraran karar, Mista Haroon ya ce: “Matata ba ta bi shawarar da wannan kotu ta ba ta ba don samar da damar zaman lafiya ya ci gaba ta hanyar amincewa da aiwatar da aikinta na matar aure.

Sai dai, Afsat ba ta halarci zaman kotun ba lokacin da aka kira ta kuma babu wanda ya wakilce ta a kotun.
Shugaban kotun, Cif Ademola Odunade, ya gargadi Haroon da ya kara hakuri.
“Kotu za ta yi aiki tare da danginta don warware matsalar cikin ruwan sanyi,” inji shi.
Mista Odunade ya daga karar zuwa ranar 17 ga watan Mayu don ci gaba da sauraran karar.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ba da rahoton cewa Haroon a watan Fabrairu ya nemi a raba aurensa mai tsawon shekaru 52 saboda kuntata masa kan hakkinsa na aure da kuma barazana ga rayuwarsa.
A cikin karar, ya yi zargin cewa Afsat na matukar son korarsa a makwanci tare da garkame kofa.

Ba zan kuma iya jure irin wannan halin ba. Mafi munin har yanzu, ita da danginta suna son ganin baya na.
Afsat tayi yunkurin soka min wuka. Tana lalata yaranmu guda shida. Ta juya musu tunani zuwa hantarata,” in ji shi.
Afsat a cikin amsarta, ta ki amincewa da bukatar rabuwa.
Farfesa yana aikata lalata. Ba zan iya yin komai da shi ba saboda ya kwanta da matan amininsa har mata uku.
Maigidana, Haroon ya kwanta da matan uku na mutumin da ke tsayawa a matsayin mai shiga tsakani a duk lokacin da muke da matsala,” in ji ta.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button