Tinubu dan gida ne a Katsina – Inji Sarkin Katsina
Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmunini Kabir Usman ya ayyana tsohon Gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan Katsina.
Sarkin yayi wannan furucin ne lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga ta ‘yan Arewa dake goyon bayan takarar Tinubu ta Shugabancin Najeriya watau Arewa Organizations Movement For Asiwaju (AROMA).
Sarkin na Katsina ya bayyana cewa fiye da shekaru 30 da suka gabata, tsohon Gwamnan jihar Legas din ya na dan kyakkyawar
alaka da masarautar tun lokacin mahaifinsa, Alhaji Muhammadu Kabir Usman don haka zai bayar da dukkan goyon bayan sa ga tafiyar siyasar sa.
Sarkin ya cigaba da cewa a bisa al’ada baya ganin mutane ranar Juma’a amma saboda alakar tawagar da masarautar ya sa dole ya saurare su.
Tun da farko, Shugaban tawagar kuma tsohon Sanatan shiyyar Katsina ta Kudu, Sanata Abu Ibrahim ya bayyana cewa sun je wurin Sarkin ne domin girmamawa ga masarautar tare da neman albarkar sa a bisa gurin da suka sa a gaba.
Sources: Katsina