Sakamakon Kungiyar Izala akan Dr Jalo Jalingo kan Maganar iyayen Annabi s.a. w
Sakamakon Kungiyar Izala akan Dr Jalo
Hotuna: Jibwis NigeriaAsakamakon zaman da shugabanni da manyan maluma na qungiyar Jamatu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta qasa suka gabatar a ofishin shugaban qungiyar na qasa Sheikh Abdullahi Bala Lau tare da shugaban malaman qungiyar ta qasa, Dr. Ibrahim Jalo a sakateriyar qunyar ta qasa anan Abuja, ranar Laraba 5/01/2022.
Qungiyar ta fidda matsaya kamar haka:
i Qungiyar ta bukaci Dr. Jalo da ya dakatar da tattauna wannan matsala ko rubutu akanta a shafin yanar gizo domin wannan matsala, lamari ne da ya shafi maluma da daliban ilimi. Kawota cikin al’umma ba zai haifar da komi ba sai rudani da rashin fahimta;
ii Qungiya ta ja hankalin dukkan maluman da ke qarqashin ta da cewa kafin su kawo wata baquwar matsala ta addani ko fatawa, da su fara gabatar da ita a gaban majalisa don tattaunawa a ilmance da samu matsaya kafin yadata cikin al’umma don kaucewa haddasa rudani da rashin fahimta;
iii Qungiyar tayi kira ga dukkan yan social media da ke qarqashin ta da su dakatar da yada wannan matsala a social media, kuma su janye ta daga shafukan su;
iv Qungiyar tayi kira ga al’ummar qasa da su mayar da hankalin su wajen addu’oin neman zaman lafiya da tsaro, wanda shi ne babban lamarin da yadami wannan qasa a yau;
v Daga qarshe muna addu’a Allah ya qara mana son Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam (SAW) Ya kuma hadamana kan maluman mu bisa Qur’ani da sunnah.
JIBWIS NIGERIA